Dandalin Siyasa
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Gasar Cin Kofin Afrika ta CAF
A ranar 21 ga watan Janairu ne aka fara gudanar da gasar cin kofin Afrika a kasashen Gabon da E/Guinea, inda kasashen Afrika 16 zasu haska a gasar, kuma wannan ita ce gasa mafi girma a Nahiyar Afrika. Bashir Ibrahim Idris, tare da bakinsa sun tattauna game da muhimmaci da tasirin gasar ga Afrika.28/01/201221:29 -
Yajin aiki a Najeriya
An kwashe tsawon mako guda, kungiyoyin kwadago, da fararen hula suna jagorantar gudanar da yajin aikin, gama-gari, domin adawa da matakin Gwamnatin kasar, na cire tallafin mai, abinda ya sa farashin man ya yi tashin goran zabbi.A cikin wannan shirin, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da bakin sa, game da yajin aikin, da kuma illar da ya yi wa kasar.14/01/201221:37 -
Karin Farashin Mai a Najeriya
Yanzu haka a Najeriya ana ci gaba da zanga-zanga, yayin da kungiyar kwadago ta kira yajin aikin gama-gari, sakamakon cire tallafin man fetur da Gwamnatin kasar ta yi, abinda ya kai ga ana sayar da man akan farashin sama da naira 140, maimakon naira 65 da ake sayar da shi ada.07/01/201222:58 -
Harin bom na ranar Kirsimeti a madalla
A KARSHEN makon da ya gabata ne aka gudanar da bikin krismati a duniya, sai dai bikin na bana ya bar baya da kura a Nigeria, sakamakon hare haren da suka yi sanadiyar mutuwar mutane sama da mutune 50, abinda ya harzuka shugaban kungiyar Kristocin kasar, wanda ya shaidawa shugaban kasa cewar, zasu umurci mabiyansu su kare kansu.A cikin wanna shirin, Bashir Ibrahim Idris, tare da bakin sa, sun tattauna kan hare haren, da kuma abinda zai haifar.01/01/201222:00 -
Sauyi a Korea ta Arewa bayan Mutuwar shugaba Jong-Il
A ranar 17 ga watan Disemba ne hukumomin kasar Korea ta Arewa, suka sanar da mutuwar shugaban kasa Kim Jong-Il, wanda ya yi kaurin suna a kasashen duniya, bayan yin fito na fito da shugabannin duniya akan shirin kasarsa na Makamashin Nukiliya.A cikin wannan shirin, Bashir Ibrahim Idris tare da bakin sa, sun tattauna kan wannan sauyi da aka samu a kasar.24/12/201121:01 -
Shirin samar da ‘Yan sandan Jahohi a Najeriya
Matsalar Tsaro a Najeriya, na ci gaba da zama barazana ga shugabannin kasar, abinda ya sa wasu Gwamnonin Jahohi suka bayyana fatarsu na samun ‘Yan Sandan Jihohi. A cikin wannan shirin, Bashir Ibrahim Idris tare da bakin shirin, sun tafka mahawara game da wannan bukatar, inda suka tattauna amfanin samar da ‘Yan sandan, da kuma akasin haka.17/12/201120:05 -
Taron samar da zaman lafiya a yankin arewacin Najeriya
Arewacin Najeriya, na daya daga cikin Yankin da ya fi hadarin zama a yau, saboda matsalar tsaro, rikicin addini da kabilanci da kuma hare haren bama bamai da ke tashi a yankin day a kai ga rasa dimbin rayuka.10/12/201121:10 -
Samar da Man Fetir a Jamhuriyyar Nijar
A cikin Wannan mako ne Jamhuriyyar Nijar ta kaddamar da matatar man fetir, matakin farko da zai bai wa kasar damar amfana da arzikin man da Allah ya wadata kasar da shi.03/12/201120:13 -
Barazanar Birtaniya akan Iran
A Shirin Duniyarmu a yau ya tattauna matakan da Kasar Britaniya, ta bayyana dauka, domin daukar matakan soji kan kasar Iran, saboda taurin kanta a shirinta na samun makamin nukiliya, ganin yadda taki amincewa da umurnin dakatar da shirin, kamar yadda Sakataren harakokin wajen kasar, William Hague ya bayyana a Brussels, amma matakin ya samu suka daga Jamus da Faransa.26/11/201120:23 -
Gargadin Amurka na kauracewa Abuja
Kamar kullum Shirin “Duniyarmu A Yau” yakan tattaunawa ne da ‘yan jarida masu sa ido ga lamurran da suka shafi duniya baki daya.Shirin kuma ya diba wani gargadi ne da Kasar Amurka da Canada suka yi wa ‘Yan kasashensu don kauracewa birnin Abuja a kwanan baya, saboda wani rahotan asiri da suka ce sun samu na shirin kai hari birnin.12/11/201120:01 -
Matsalar noma a kasashen Africa
A kwanan nan ne Hukumar da ke kula da noma da samar da abinci ta Majalisar Dunkin Duniya, ta yi gargadi kan yadda attajirai da kuma kanfanoni ke sayen filayen noma a kasashe masu tasowa, abinda ke jefa manoman cikin talauci da kuma rage hanyoyin samar da abinci.A cikin wanan shirin, Bashir ibrahim Idris ya tattauna da wasu Yan Jaridu kan matsalar da kuma yadda za’a shawo kanta.16/10/201119:38 -
Zaben Shugaban kasa a Kamaru
A ranar Lahadi ne 9 ga watan Octoba aka gudanar da zaben shugaban kasar Kamaru, inda shugaba Paul Biya, da ya kwashe shekaru 29 yana shugabancin kasar, zai fafata da wasu Yan takara 22.A cikin shirin Duniyarmu A Yau, Bashir Ibrahim Idris ya tattauana da wasu ‘Yan Jarida kan zaben, da kuma rawar da ‘Yan adawa zasu taka.07/10/201120:29
Dandalin Siyasa
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.