Dandalin Siyasa
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Batun dage ranar Zabe a Najeriya
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne game da matakin dage ranar babban zabe a Najeriya daga 14 ga watan Fabrairu zuwa 28 ga watan Maris.17/02/201521:27 -
Zaben 2015: Dambarwar siyasa a Najeriya
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne akan dambarwar siyasa a Najeriya musamman zaben 2015 da kasar ke shirin gudanarwa a watan Fabrairu. Shirin ya mayar da hankali akan yakin neman zaben Shugaban kasa.05/02/201520:02 -
APC da PDP sun tabbatar da 'Yan takararsu
Shirin Dandalin Siyasa ya yi nazari ne game da 'Yan takarar da manyan Jam'iyyun siyasa a Najeriya suka tsayar domin wakiltarsu a babban zaben shekara mai zuwa. PDP mai mulki ta tabbatar da shugaba Goodluck Jonathan a matsayin dantakarta, yayin da kuma APC mai adawa ta tsayar da Janar Muhammadu Buhari.17/12/201420:10 -
Tambuwal a dambarwar APC a Najeriya
Shirin Dandalin Siyasa ya diba dambarwar siyasar Jam'iyyar APC a Najeriya musamman game da sayen fom din takarar shugaban kasa da Kakakin Majalisa Aminu Waziri Tambuwal ya saya domin fafatawa a zaben 2015, lamarin da ya canyo cece-kuce tsakanin 'ya'yan Jam'iyyar.26/11/201420:30 -
Jonathan ya yanki tikitin Takara, Tambuwal ya fice PDP
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna da 'Yan siyasar arewa da suka sayawa Shugaban Najeriya tikitin sake tsayawa Takarar Shugaban kasa, haka kuma shirin ya tattauna da Aminu Waziri Tambuwal Kakakin Majalisa akan dalilin ficewarsa PDP zuwa Jam'iyyar adawa ta APC.03/11/201420:20 -
Duniyarmu A Yau: Rikicin siyasar jihar Taraba
Yunkurin da wasu ke yi na ganin an danka ragamar mulkin jihar Taraba a hannun gwamna Danbaba Suntai da ke fama da rashin lafiya, da tsarewar da jami'an tsaro suka yi wa tsohon gwamnan Gombe Danjuma Goje da kuma aniyar sakewa tsayawa takarar neman shugabancin Najeriya da Alhaji Atiku Abubakar ya yi a mokon jiya, na daga cikin muhimman batutuwan da ke kunshe a wannan shiri tare da Bashir Ibrahim Idris.22/09/201422:04 -
Dambarwar Siyasar Jam'iyyar PDP a Zamfara
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne akan dambarwar Siyasar shugabancin Jam'iyyar PDP da ke adawa a Jihar Zamfara, inda a A ranar 2 ga watan Satumba ne za'a gudanar da zaben shugabancin Jam'iyyar domin zaben wanda zai jagoranci Jam'iyyar wajen tunkarar Jam'iyya APC da ke mulki a Jihar a zaben 2015.03/09/201422:00 -
Duniyarmu A Yau: An kammala taron kasa a Najeriya
Batun Kammala taron kasa a Najeriya da sauran batutuwa na siyasa a Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar, na daga cikin abubuwan da shirin Dandalin Siyasa na wannan mako ya kunsa tare da Bashir Ibrahim Idris.16/08/201419:58 -
Dandalin Siyasa: Siyasa da tabarbarewar tsaro a Najeriya
A daidai lokacin da 'yan Najeriya suka soma shirye-shirye dangane da zabubukan da za a gudanar a cikin shekara mai zuwa, a nasu bangare kuwa manazarta sun soma nuna shakku ne a game da yiyuwar samun cikas sakamakon yawaitar hare-haren ta'addanci a cikin kasar. Wannan ne Bashir Ibrahim Idris ya yi mayar da hankali a cikin shirinsa na Dandalin Siyasa na wannan mako.04/08/201421:01 -
Dambarwar Siyasar Adamawa
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne game da dambarwar Siyasar Jihar Adamawa a Najeriya inda 'Yan Majalisar Jihar suka tsige Gwamna Murtala Nyako da ke takun-saka da Shugaba Jonathan bayan gwamnan ya canza sheka daga Jam'iyyar PDP zuwa APC mai adawa.20/07/201421:50 -
Siyasa da Matsalar Tsaro a Najeriya
Shirin Dandalin Siyasa ya diba batun matsalar tsaro ne a Najeriya da kuma yadda siyasa ke tasiri ga matsalar musamman dangane da batun dage zabe saboda matsalar tsaro.28/05/201421:31 -
Matsalar Tsaro a Najeriya
Bisa ga dukkan alamu, matsalar tsaro na ci gaba da tabarbarewa a tarayyar Najeriya, inda ake kashe mutanen da ba su ji ba su kuma gani ba. Yayin da dakarun kasar ke kokarin shawo kan matsalar a sassa daban daban, 'yan siyasa na can suna cecekuce kan yadda za a shawo kan matsalar. Yau akan wannan batu shirin Dandalin Siyasa zai ta'allaka.26/04/201421:25 -
Siyasar Jahar Kano
Shirin Dandalin Siyasa ya yi bayani akan Ziyarar Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a Jahar Kano musamman dambarwar siyasa tsakanin Kwankwaso da Gwamnatin PDP a Tarayya.19/04/201420:35 -
Gwamnatin Issoufou ta cika shekaru uku
Shirin Dandalin Siyasa ya kai ziyara ne Jamhuriyyar Nijar bikin cika shekaru da Muhamadou Issoufou ya yi kan karagar mulki.13/04/201420:51 -
Ci gaba da Dokar ta-baci a wasu jahohin arewacin Najeriya
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne Dattawan arewacin Najeriya daga yankin arewa maso gabacin Najeriya da ke cikin dokar ta-baci. Shirin kuma ta tabo zargin Gwamnonin Jahohin da shugaban kasar Goodluck Jonathan ya yi.06/04/201421:12
Dandalin Siyasa
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.