Dandalin Siyasa
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Rikicin Kasafin Kudi a Najeriya
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna kan sabanin da ake samu tsakanin bangaren Zartarwa da Majalisar Dokokin Najeriya a game da Kasafin Kudi wanda har yanzu Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ki sanya wa hannu. Sannan shirin ya tabo rikicin Siyasa a Nijar inda ake ta cece-kuce kan yawan Ministocin da Shugaba Mahamadou Isooufou ya nada.18/04/201620:23 -
Yunkurin kifar da gwamnatin Issoufou na Nijar
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne kan dambarwar siyasar Nijar inda Shugaban kasar Mahamadou Issoufou ya ce an yi yunkurin yi ma sa juyin mulki. Sannan Shirin ya tabo siyasar Najeriya.21/12/201521:35 -
Rikicin Siyasar Kogi a Najeriya
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne game da dambarwar siyasar Jihar Kogi inda ake takaddama kan wanda zai gaji Prince Abubakar Audu na APC da ya rasu kafin kammala zaben Jihar. Shirin ya kuma leka siyasar Nijar.30/11/201520:42 -
Komawar Hama Amadou Nijar
Shirin Dandalin siyasa ya leka Jamhuriyyar Nijar inda Hama Amadou babban mai adawa da Mahammadou Issoufou ya dawo gida Nijar ya shafe lokaci yana buya a Faransa kan tuhumar da ake masa game da mallakar jarirai ba kan ka'idar dokar kasa ba. Shirin kuma ya yi bayani akan dambarwar siyasar Jihar Taraba a Najeriya. Shirin ya tabo batun taron PDP mai adawa da ta nemi afuwar 'Yan Najeriya.16/11/201520:55 -
Dambarwar siyasar Nijar
Shirin Dandalin Siyasa ya yi bayani game da dambarwar siyasar Jamhuriyyar Nijar inda ‘Yan adawa ke korafi akan rigistar masu kada kuri’a da tare kuma yin kira a yi garanbawul ga kotun zabe. Shirin ya tattauna da tsohon shugaban kasar Mahammane Ousmane.10/11/201521:23 -
Shirin dandalin Siyasa na wannan mako zai ci gaba kamar yadda ya saba, da tattaunawa kan siyasar Nijeria
a wannan mako Bashir Ibrahim Idris ya tattauna kan rashin ja gaba da ake ganin jam'iyar PDP mai adawa a Najeriya ke fuskanta, bayan da mulki ya subuce daga nannuta ya kuma fada a hannun jam'iyar APC. A sha sauraro lafiya27/09/201520:58 -
Matsalar tsaro a zamanin Buhari a Najeriya
Shirin Dandalin Siyasa ya mayar da hankali ne akan matsalar tsaro a Najeriya musamman game da hare haren kunar bakin wake da Mayakan Boko suka tsawalla a zamanin Mulkin Muhammadu Buhari wanda ya sha alwashin kawo karshen ayyukan Kungiyar.13/07/201520:53 -
Farfesa Attahiru Jega ya kammala aikinsa a hukumar zaben Najeriya
Shirin Dandalin Siyasa a wannan mako, Bashir Ibrahim Idris ya mayar da hankali ne kan shugaban Hukumar Zaben Najeriya INEC Farfesa Attahiru Jega, wanda ya kawo karshen aikinsa a hukumar cikin makon da ya gabata.05/07/201520:49 -
Rikicin zauren Majalisar wakilan Najeriya
Shirin dandalin Siyasa a wannan lokaci ya mayar da hankali ne akan rikici da aka tafka a zauran Majalisar kasar, rikici da ya kai ga baiwa hamata Iska tare da Bashir Ibrahim Idris.28/06/201520:30 -
Sabbin gwamnoni sun tarar da dimbin basusuka a Najeriya
Shirin Dandalin Siyasa na wannan mako, ya mayar da hankali ne a game da irin bashin da gwamnonin wasu jihohi ke ikirarin cewa sun gada daga wadanda suka gabace su.Bashir Ibrahim Idris ya yi dubi a game da wannan batu, kuma shi ne babban maudu'in shirin na wannan mako.20/06/201520:30 -
Rikicin zabe a Majalisun Tarayyar Najeriya
Rikici a Majalisun Tarayyar Najeriya, sakamakon yadda wasu 'yayan jam'iyyar APC mai mulkin kasar suka ki bin umurnin jam'iyyar na zaben wadanda ta tsayar takarar neman shugabancin Majalisun biyu.A cikin wannan shiri na Dandalin Siyasa, Bashir Ibrahim Idris ya yi mana dubi dangane da wannan badakala.14/06/201521:48 -
Kalubalen da ke gaban Buhari
Shirin Dandalin Siyasa ya yi nazari ne game da manyan kalubalen da ke gaban sabon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.11/06/201521:35 -
Bikin rantsar da Buhari a Najeriya
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne game da bikin Rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin sabon shugaban Najeriya.03/06/201520:37 -
Shugaban PDP Ahmed Mu'azu ya yi murabus
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna kan rikicin Jam'iyyar PDP da ta sha kaye a zaben 2015 a Najeriya. Shirin ya mayar da hankali game da murabus din shugaban PDP Ahmed Mu'azu.27/05/201520:36 -
Faduwar PDP a zaben Najeriya
Shirin Dandalin Siyasa ya yi nazari ne game da yadda Jam'iyyar PDP ta sha kaye a zaben Najeriya bayan ta shafe shekaru 16 tana shugabanci a kasar. Sannan shirin ya yi tsokaci akan nasarar da Janar Muhammadu Buhari ya samu.28/04/201520:52
Dandalin Siyasa
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.