Dandalin Siyasa
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Shari'ar Akingbola na Najeriya a London
A makon nan ne wata kotu a birnin London, ta samu tsohon shugaban bankin Intercontinental, Erastus Akingbola, da laifin almundahana da kudade har Dala biliyan 165, inda bankin ya umurce shi day a mayar da kudaden.04/08/201221:15 -
Mandela ya cika shekaru 94
A shekarar 2012 ne Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela ya yi bukin cika shekaru 94 a duniya cikin koshin lafiya, kodayake tsohon shugaban ya yi fama da rashin lafiya kawo yanzu. Shirin Duniyarmu A Yau ya yi bayani ne game da Tsohon shugaban.22/07/201221:40 -
Zaben Shugaban kasa a Masar
Bashir Ibrahim Idris tare da bakin Shirinsa na Duniyarmu A Yau sun tattauna akan Zaben Shugaban kasa a Masar.23/06/201219:51 -
Hadarin Jirgin Dana a Najeriya
A shirin Duniyarmu A Yau Bashir Ibrahim Idiris tare da Abokan shirin shi sun tattauna game da hadarin Jirgin Dana da aka samu a Jahar Lagos Tarayyar Najeriya.10/06/201220:22 -
Taron Sarakunan Najeriya game da matsalar tsaro da Cin hanci
Shirin ya yi bayani game da sakamakon taron Sarakunan Najeriya wadanda suka tattauna batutuwan da ke addabar kasar tare da fito da hanyoyin magance matsalolin musamman Cin hanci da Rasha da matsalar Tsaro.09/06/201220:09 -
Bukin Cika shekaru 13 da mulkin Demokradiya a Najeriya
A ranar 29 ga Watan Mayu ne aka yi bikin cika shekaru 13 a Najeriya, da komawa mulkin Demokradiya, kuma dai dai da cika shekara guda ga Gwamnatin Goodluck Jonathan.Wasu suna zargin sojoji sun hana kawo ci gaba a Najeriya, saboda kwashe shekaru da dama suna mulki, wasu kuma suna zargin ‘Yan Siyasa da matsalolin da suka addabi kasar, musamman cin hanci da rashawa, inda suke zargin jami’an gwamnati da sace kudaden da ake warewa dan yi wa talakawa aiki.02/06/201223:29 -
Matsalar Yunwa a Nahiyar Afrika
A wani Rahoton Hukumar kula da Ci gaba ta Majalisar Dinkin Duniya, Rahoton ya bayyana cewa duk da ci gaban tattalin arzikin da Afrika ta samu a cikin shekaru goma da suka gabata, Yankin na fama da matsalar yunwa.20/05/201220:50 -
Zaben Faransa Zagaye na Biyu
A Ranar 6 ga Watan Mayu ne aka gudanar da zaben shugaban kasar Faransa zagaye na Biyu tsakanin shugaba Nicolas Sarkozy, Francois Hollande bayan kammala zagayen Farko Hollande yana kuri;u kashi sama da 28, yayin da shugaba Nicolas Sarkozy ya zo na biyu da sama da kashi 27. A cikin Duniyarmu A Yau shirin, Bashir Ibrahim Idris tare da abokan shirin sun tattauna game da dambarwar Siyasar Faransa kafin zagaye na biyu.05/05/201222:03 -
Nasarar Macky Sall a Senegal
A farkon wannan mako ne aka gudanar da zaben shugaban kasa, zagaye na biyu a kasar Senegal, tsakanin shugaba Abdoulaye Wade, wanda ke rike da karagar mulki da Macky Sall, shugaban ‘Yan adawar kasar. Tuni sakamakon zaben ya nuna cewa, shugaba Wade ya sha kaye, yayin da Macky Sall da ya samu goyan bayan sauran ‘Yan takaran, ya zama zababben shugaban kasa.28/04/201220:40 -
Zaben Shugaban kasar Faransa
A ranar 21 ga watan Afrilu ne aka gudanar da zaben shugaban kasar Faransa, inda ‘Yan takara Goma suka fafata cikin su har da shugaba mai ci, Nicolas Sarkozy, don samun nasara. A karon farko a tarihin zaben Faransa, an samu sabon salon siyasa inda shugaba mai ci ke fuskantar kalubale, domin Sarkozy yana fuskantar kalaubale daga shugaban Yan adawa, Francois Hollande na Jam’iyyar gurguzu ta Socialist. A cikin shirin, Bashir Ibrahim Idris tare da abokan shirinsa sun duba zaben da kuma matsalolin da kan iya yi wa shugaba Sarkozy tarnaki.21/04/201220:20 -
Zaben shugaban Babban Bankin Duniya
A ranar 16 ga Watan Afrilu ne ake nada sabon shugaban bankin Duniya, daya daga cikin manyan hukumomin kudade na duniya. Kuma Jim Yong Kim ne ya lashe zaben bayan fafatawa da Ngozi Ikonjo Iweala ta Najeriya.14/04/201223:18 -
Juyin mulkin kasar Mali
Shirin Duniyarmu A Yau da Bashir Ibrahim Idiris ke jagoranta tare da wasu 'Yan Jarida ya yi tsokaci ne game da juyin mulkin da sojojin kasar Mali suka yi wa gwamnatin Farar hula ta Amadou Toumani Toure a ranar 21 ga watan Maris.24/03/201221:00 -
Harin Kano a Najeriya
Akwai hare haren bama bamai, da kuma musayar wuta tsakanin wasu ‘Yan bindiga da jami’an tsaro da aka samu a birnin Kano, harin da ya tada hankalin daukacin Najeriya da ma duniya baki daya, wanda ya lakume rayukan mutane 186, kamar yadda rundunar ‘Yan Sandan Jihar ta tabbatar. A cikin wannan shirin, Bashir Ibrahim Idris tare da bakin shi sun tattauna game da hare haren, da kuma yadda za’a kawo karshensu.28/02/201221:50 -
Talauci a Najeriya
Hukumar Kididdiga a Najeriya ta fitar da wani rehoto wanda ke cewa mutanen da ke rayuwa kasa da Dalar Amurka suna ci gaba da karuwa tun a shekarar 2004 duk da ci gaban tattalin arzikin da ake samu a kasar ta bangaren man fetur. Shugaban hukumar Yemi Kale, yace akwai ci gaban tattalin arziki da aka samu a Najeriya amma Talauci sai ci gaba da karuwa yake yi a cikin kasar duk shekara.18/02/201221:34 -
Abdul Katako yace shaidar karya ya bayar a shari’ar Al Mustapha
A ranar 30 ga wata watan Janiru ne wata kotu a Najeriya, ta yanke wa Manjo Hamza al Mustapha, tsohon dogarin Janar Sani Abacha hukuncin kisa, kan samun shi da hannu wajen kashe Kudirat Abiola, bayan an kwashe shekaru 14 ana tafka shari’a.Kwanaki bayan yanke hukuncin, sai ga Muhammad Abdul Katako, daya daga cikin shaidun da suka bada shaida kan zargin da ake wa al Mustapha, ya fito fili yana cewa, shaidar zur ya bayar, kuma yana neman gafarar al Mustapha.11/02/201220:44
Dandalin Siyasa
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.