Nijar ta ce Faransa ta jibge makamai a wasu kasashe kusa da ita don yakar ta
Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta zargi Faransa da tara makamai tare da jibge dakarunta a wasu kasashe da ke makwaftaka da kasarsu da zummar kai musu hari.
Wallafawa ranar:
A ranar Asabar ce kakakin gwamnatin sojin Nijar, Kanar Manjo Amadou Abdramane ya bayyana a wata sanarwa cewa Faransa na ci gaba da jibge dakaru a wani Shirin da take yi da kunggiyar ECOWAS don kai wa kasar hari, inda ya ce ta tara jiragen yaki, da jirage masu saukar ungulu, da kuma motoci masu sulke guda 40 a kasashen Ivory Coast da Jamhuriyar Benin.
Kasar da ke yankin Sahel ta shiga takun saka da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka, wato ECOWAS tun bayan da kungiyar ta yi barazanar yin amfani da karfi idan diflomasiyya ta gaza, a kokarin da take na maido da Mohamed Bazoum kan mulki.
A ranar 3 ga watan Agusta ce gwamnatin sojin Nijar ta soke yarjejeniyar soji da ke tsakaninta da Faransa, wadda ke da dakaru kimanin dubu 1 da dari 5 a kasar da ta jibge don taimakawa a yakin da ake da ta’addanci.
Dangantaka tsakanin Faransa da Jamhuriyar Nijar ta yi tsami tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yuli.
Faransa ta ki amincewa da gwamnatin sojin Nijar, inda ta ayyana ta a matsayin haramtacciya, tana kuma kira su mayar da Bazoum karagar mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu