Isa ga babban shafi
labarin aminiya

Muna fatan kulla yarjejeniya da ECOWAS - Sojin Nijar

Firaiministan da sojoji suka nada a Jamhuriyar Nijar ya ce yana fata za su kulla yarjejeniya da ECOWAS “nan da kwanaki masu zuwa” duk da barzanar da kungiyar ta yi na yin amfani da karfin soji a kansu bayan juyin mulkin watan Yuli.

Firaministan Nijar a mulkin soji M. Ali Mahaman Lamine Zeine.
Firaministan Nijar a mulkin soji M. Ali Mahaman Lamine Zeine. AFP - -
Talla

Ali Mahaman Lamine Zeine ya shaida wa wani taron manema labarai ranar Litinin cewa ana gudanar da “tuntuba” domin janye sojojin Faransa daga kasar “cikin gaggawa”.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da dubban ’yan kasar suke ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman Faransa ta fita daga Nijar.

“Ba mu daina tuntubar ECOWAS ba, muna ci gaba da tuntuba. Muna fata za a cimma yarjejeniya nan da kwanaki masu zuwa,” in ji Firaiminista Ali Mahaman Lamine Zeine a taron manema labarai da ya gudanar a Yamai.

Sai dai ya yi gargadi cewa sojojin ba za su amince da duk wani yunkuri na mayar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum kan mulki.

“A shirye muke a koyaushe don fuskantar hari. Mun shirya. Yakin ba zai kasance bai adalci ba. Mun sha alwashin kare kasarmu idan aka kawo mana hari,” in ji Zeine.

Sojojin sun ce sun cika dukkan sharudan da ECOWAS ta sanya musu game da yiwuwar mika mulk ga gwamnatin farar-hula.

“ECOWAS ta nemi abubuwa da suka hada ganin shugaban kasa [Bazoum], da sanya wa’adin mika mulki ga farar-hula.

“Tsohon shugaban Najeriya da mai alfarma Sarkin Musulmi sun zo nan sau biyu, haka kuma manyan malamai ma sun zo. Kuna gani ni na raka su suka ga Bazoum,” a cewarsa.

Firaiminista Zeine ya ce su gaya wa ECOWAS cewa ba za su wuce shekara uku a kan mulki ba don haka bai kamata a yi wata fargaba ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.