Isa ga babban shafi

Gwamnatin sojan Nijar ta yi tir da tsoma bakin Faransa kan kasar

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta zargi Faransa da yi mata zagon kasa, na goyon bayan hambararren shugaban kasar a daidai lokacin da masu zanga-zangar suka yi dafifi a kusa da wani sansanin Faransa da ke wajen Yamai babban birnin kasar.

Shugaban gwamnatin sojin Nijar kenan, Abdourahmane Tchiani.
Shugaban gwamnatin sojin Nijar kenan, Abdourahmane Tchiani. AP
Talla

A ranar 26 ga watan Yuli ne wasu jami'an shugaban suka tsare shi, wanda zabensa a shekarar 2021 ya haifar da fatan samun kwanciyar hankali a kasar mai fama da rikici.

Kalaman shugaban Faransa Emmanuel Macron na goyon bayan Bazoum "sun zama karin tsoma baki a harkokin cikin gidan Nijar," in ji kakakin gwamnatin Kanar Amadou Abdramane a wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar.

Kasar da ke yankin Sahel, na fama da rashin jituwa tsakaninta da kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka, wadda ta yi barazanar shiga tsakani ta hanyar soji idan matsin lamba ta diflomasiyya na mayar da zababben Bazoum kan mukaminsa ya gaza samuwa.

A ranar Litinin, Macron ya yi kira ga daukacin kasashen yankin da su aiwatar da manufofin da suka dace.

Faransa, in ji shi, tana goyon bayan matakin diflomasiyya na ECOWAS, kuma idan ta yanke shawara, matakin soja, aka kasar, za su iya mika tayin hadin gwiwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.