Isa ga babban shafi

Nijar ta bai wa jakadan Faransa sa'o'i 48 ya fice daga kasar

A wata wasika daga Ofishin Ministan Harakokin Wajen Jamhuriyar Nijar, Majalisar sojin kasar ta bukaci Jakadan Faransa Sylvain Itte da ya fice daga kasar cikin sa'o'i 48.

Wasu daga cikin masu goyon bayan Faransa ta fice daga Jamhuriyar Nijar
Wasu daga cikin masu goyon bayan Faransa ta fice daga Jamhuriyar Nijar © AFP
Talla

A wata wasika da ya aikewa jakadan Faransa a jamhuriyar Nijar, ministan harkokin wajen kasar Bakary Yaou Sangare ya mika  yabawa mahukuntan Faransa tare da yin amfani da damar wajen sanar musu dalilan korar jakadan daga Yammai.

Gwamnatin Nijar tace daukar matakin ya biyo bayan kin amsa gayyatar hukumomin Nijar domin tattauna akan dalilin da ya sa tsohuwar Jakadiyyar Nijar ta taka na kin sauka daga mukamin ta da kuma ganawa da Ministan harkokin wajen Faransa bayan an bata umarni.

Sanarwar tace kin amsa gayyatar da ma'aikatar harkokin wajen kasar da 'yan Nijar suka yi masa domin ganawa da shi a yau Juma'a 25 ga watan Agusta, 2023 da misalin karfe 10:30 na safe da kuma wasu ayyukan da gwamnatin Faransa ta yi wanda ya saba wa muradun Jamhuriyar Nijar na daga cikin dalilan daukar mataki.

Alamomin Ofishin jakadancin Faransa a birnin Yamai
Alamomin Ofishin jakadancin Faransa a birnin Yamai © AFP

Hukumomin Nijar din sun yanke shawarar janye amincewarsu ga jakadan Faransa Sylvain Itte tare da neman ya fice daga kasar ta Nijar cikin sa'o'i 48.

Ma'aikatar harkokin waje ta Jamhuriyar Nijar ta yi amfani da wannan damar wajen jaddada girmamawar ta ga hukumomin Faransa a cikin wasikar da suka rubuta.

Zanga-zanga a harabar ofishin jakadancin Faransa a Nijar
Zanga-zanga a harabar ofishin jakadancin Faransa a Nijar © REUTERS/Stringer

Ya zuwa wannan lokaci,hukumomin kasar Faransa ba su mayar da martani ko fitar da sanarwa a kai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.