Isa ga babban shafi

Sojojin Nijar na shirin fara tattaunawa da Rasha

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun sanar da shirinsu na fara tattaunawa da Rasha don samar da masalaha da kuma kawo karshen rikicin da ya biyo bayan juyin mulkin da suka yi.

Wasu daga cikin sojojin Nijar da suka yi juyin mulki a ksar.
Wasu daga cikin sojojin Nijar da suka yi juyin mulki a ksar. REUTERS - STRINGER
Talla

Firaministan Jamhuriyar Nijar Ali Lamine Zeine ne ya bayyana hakan bayan ziyarar da ya kai kasar Chadi.

Wannan na zuwa ne bayan da Rasha da Amurka sun bukaci mahukuntan yankin su dauki matakin kawo karshen matsalolin da suka taso.

Wutar rikicin na kara zafi, tun bayan da kasashen duniya da kuma kungiyoyi ke kara matsa lamba kan sojoji da su mayar da mulki ga Mohamed Bazoum da suka kwata daga hannunsa.

A yanzu dai, ana jiran a ga irin matakin da za a cimma wajen taron manyan hafsoshin kasashen ECOWAS a birnin Accra da ke gudana a wannan Alhamis kan yiwuwar afka wa Jamhuriyar Nijar da yaki ko kuma akasin haka.

Tun bayan juyin mulkin, an ga irin yadda ‘yan kasar suka rika  nuna goyon baya ga sojoji, tare da adawa kasancewar Faransa a kasar da kuma bukatar Rasha ta shiga cikin lamarinsu da kuma kai musu dauki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.