Isa ga babban shafi

EU ta goyi bayan ci gaba da zaman jakadan Faransa a Nijar duk da barazanar Soji

Kungiyar tarayyar Turai ta bayyana cikakken goyon baya ga jakadan Faransa a Nijar Sylvain Itte bayan kin amincewarsa da fita daga kasar duk da wa’adin da sojojin da suka yi juyin mulki suka dibar masa.

Shugaban mulkin Sojin Nijar Abdourahamane Tchiani.
Shugaban mulkin Sojin Nijar Abdourahamane Tchiani. AP
Talla

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen EU Nabila Massrali ta bayyana cewa, matakin bai wa jakadan wa’adi wata sabuwar takala ce daga sojojin da suka yi juyin mulkin na Nijar kuma hakan ba zai samar da mafita ga rikicin da suka dabaibaye kasar ba.

A cewarta, EU ba ta amince ba, kuma ba ta kallon sojojin na Nijar a matsayin halastacciyar gwamnati wanda ke nuna ba su da hurumin korar kowanne jakada.

A Juma’ar da ta gabata ne Sojojin na Nijar suka bai wa jakadan Faransa a birnin Yamai Sylvain Itte wa’adin sa’o’i 48 ya bar kasar amma kuma ya yi watsi da matakin tare da ci gaba da zama.

Tuni dai batun ya haddasa cece-kuce, inda shugaba Emmanuel Macron ya nanata cewa jakadan zai ci gaba da zama a Yamai domin sojojin ba su da hurumin korar shi.

A ranar 26 ga watan jiya ne Sojojin Nijar suka yi wa gwamnatin Mohamed Bazoum juyin mulki tare da ci gaba da tsare shi baya ga kulle duk wata kofar tattaunawa tsakaninsu da kungiyoyi dama Faransa da ke matsayin uwar goyo ga kasar.

Wannan mataki na Sojin Nijar ya haddasawa kasar fuskantar takunkumai daban-daban baya ga kulle dukkanin asusun ajiyarta da ke ketare lamarin da ya jefa al’umma a kakanikayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.