Isa ga babban shafi

Kungiyoyin farar hula sun bukaci sojojin Faransa su fice daga Nijar

Gamayyar kungiyoyin farar hula a Jamhuriyar Nijar da suka hada da M62 ta bukaci Faransa da ta janye sojojinta daga kasar da ke Yammacin Afirka.

Wani sojan Faransa a Burkina Faso
Wani sojan Faransa a Burkina Faso © MICHELE CATTANI / AFP
Talla

Abdoulaye Seydou, shugaban Gamayyar Kungiyoyin Farar Hula ta M62 a ranar Litinin din da ta gabata ya nuna adawa da kasancewar sojojin Faransa a Nijar, inda ya ce yunkurin kungiyar ba zai yi kasa a gwiwa ba har sai sojojin Faransa sun fice.

Sojojin Faransa  dubu 1 da 500 ne suka kasance a Nijar tun bayan da gwamnatin Paris ta mayar da kasar a matsayin cibiyar ayyukan da take yi a yankin Sahel a bara.

Ba za mu bai wa sojojin Faransa dakika daya ba a yankinmu da zarar wannan wa'adin ya cika, kamar yadda CNSP da kanta ta bayyana. Duk kauyuka, da garuruwan da ke kewaye za su fice tun da sojoji sun karbi mulki, in ji Abdoulaye Seydou.

A ranar 3 ga watan Agusta, sojojin da ke mulkin Nijar suka yi Allah wadai da jerin yarjejeniyoyin soja da suka kulla da Faransa, wasu daga cikinsu sun hada da wa'adin wata guda.

A 'yan watannin baya-bayan nan, kyamar Faransa na karuwa a kasashen da Faransar ta yi wa mulkin mallaka a yammacin Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.