Isa ga babban shafi

Faransa ta bukaci sojoji su tabbatar da tsaron ofishin jakadancinta dake Nijar

Faransa ta bukaci sojoji da suka yi juyin Mulki a Nijar da su tabbata sun ba da cikakken kariya da tsaron ofishin jakadancinta dake Niamey.

Masu zanga-zangar goyon bayan sojoji da suka juyin mulki a mashigin ofishin jakadancin Faransa dake Yamai. 30/07/23
Masu zanga-zangar goyon bayan sojoji da suka juyin mulki a mashigin ofishin jakadancin Faransa dake Yamai. 30/07/23 © REUTERS/Stringer
Talla

Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta bukaci gwamnatin sojin da tabbatar da cikakken tsaron ofishin jakadancinta da ke Yamai gabanin zanga-zangar da aka shirya yi a babban birnin kasar bayan juyin Mulki da sojoji su yi. Bukatar ta zo ne a daidai lokacin da Amurka ta ba da umarnin kwashe wasu ma'aikatan ofishin jakadancinta a cikin dare.

Amurka da Burtaniya

'Yan sa'o'i bayan sanarwar Amurka, Birtaniya ma ta bayyana Shirin rage ma'aikatan ofishin jakadancinta na wani dan lokaci a Yamai babban birnin Nijar.

Faransa ta bukaci jami'an tsaron Nijar da su dauki matakan da suka dace don tabbatar da cewa sun tabbatar da tsaron ofisoshi da jami’an diflomasiyyar kasashen waje, wanda tace yain haka ya zama wajibai a karkashin dokokin kasa da kasa, musamman karkashin yarjejeniyar Vienna.

Zanga-zanga

A ranar Lahadin da ta gabata magoya bayan masu juyin mulkin sun kai hari kan ofishin jakadancin Faransa da ke Yamai, inda suka cinna wuta a wajen katangarsa tare da farfasa tagogi.

Kungiyar M62 mai fafutuka da ta shirya zanga-zangar nuna goyon bayan Rasha da kin jinin Faransa, ta yi kira ga mazauna birnin Yamai da su tashi tsaye tare da mamaye filin jiragen saman kasar har sai jami'an sojan kasashen waje su fice daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.