Isa ga babban shafi

Jirgin Faransa dauke da masu barin Nijar sakamakon juyin mulki ya isa Paris

Jirgin saman Faransa mai dauke da fasinjoji 262, akasari Turawa da ya tashi daga Jamhuriyar Nijar a daren Talata ya sauka a filin tashi da saukar jiragen saman Charles de Gaulle na birnin Paris  da sanyin safiyar Larabar nan, mako guda bayan hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum da sojoji suka yi .

Wasu da suka isa birnin Paris na Faransa daga Nijar.
Wasu da suka isa birnin Paris na Faransa daga Nijar. REUTERS - STEPHANIE LECOCQ
Talla

Jirgin, wanda Faransa ta yi hayarsa, ya tashi daga Jamahuriyar Nijar  a daren Talata dauke da wadanda suka  bayyana aniyar barin kasar da sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum a makon da ya gabata.

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta ce akwai ‘yan asalin Nijar, Portugal, Habasha da Lebanon a cikin jirgin  da ya sauka, tana mai cewa ana sa ran saukar jirgi na biyu mai dauke da Faransawa, ‘yan Najeriya, Jamusawa, Amurkawa da Indiyawa da sauransu a wannan Laraba.

Ministar harkokin kasashen wajen Faransa, Catherine Colonna ta  tabbatar da isar jirgin birnin Paris, wanda ta ce daga cikin fasijojinsa, wadanda akasari Faransawa ne, akwai jarirai 12. 

Akasarin fasinjojin da suka sauka sun ce sun samu kwanciyar hankali sakamakon barin Nijar biyo bayan kwanakin da aka kwashe na zanga-zanga mai cike da tarzoma, suna mai bayyana damuwa kan halin rashin tabbas da ake ciki a kasar da suka baro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.