Isa ga babban shafi

EU ta bukaci Birtaniya ta dakatar da shirinta na maida masu neman mafaka Rwanda

Hukumar Kare Hakin bil adama ta Kungiyar Tarayyar Turai, ta bukaci Birtaniya da ta yi watsi da shirin ta na maida masu neman mafaka ‘yan Rwanda gida, inda ta ce akwai al’amura da dama da ke cike da sarkakiya kan batun.

Hukumar kare hakin bil adama ta kungiyat kasashen Turai ta bukaci Birtaniya da ta yi watsi da shirin ta na maida masu neman mafaka ‘yan Rwanda gida.
Hukumar kare hakin bil adama ta kungiyat kasashen Turai ta bukaci Birtaniya da ta yi watsi da shirin ta na maida masu neman mafaka ‘yan Rwanda gida. © Johanna Geron / Reuters
Talla

A jiya Litinin ne dai majalisar Birtaniya ta amince da dokar mai da masu neman mafaka ‘yan Rwanda gida har zuwa lokacin da za a amince da bukatarsu, a kokarin da firaministan kasar Rashi Sunak ke yi na ganin ya hana mutane yin kasada da rayuwarsu ta keta teku don tsallakawa kasar.

To sai dai shugaban Hukumar Kare Hakkin bil’adama na kungiyar EU Michael O’Flaherty, ya ce samar da dokar da kasar ta yi yaci karo da hakkin masu neman mafakar.

Sakataren harkokin cikin gidan Birtaniya James Cleverly da ministan harkokin wajen Rwanda  Vincent Biruta a lokacin wani taron manema labarai da suka yi a Kigali a ranar 5 ga watan Disambar 2023 bayan sanya hannu kan yarjejeniyar mai da masu neman mafaka
.
Sakataren harkokin cikin gidan Birtaniya James Cleverly da ministan harkokin wajen Rwanda Vincent Biruta a lokacin wani taron manema labarai da suka yi a Kigali a ranar 5 ga watan Disambar 2023 bayan sanya hannu kan yarjejeniyar mai da masu neman mafaka . AFP - BEN BIRCHALL

Birtaniya dai na daya daga cikin kasashe mambobin hukumar 46 da suka sanya hannu kan dokar kare hakkin bil’adama, don haka dole ne kasar ta yi biyayya ga umarnin kotun kare hakkin bil’adama na Turai, wacce a watan Yunin shekarar 2022 ta bada umarnin dakatar da kasar daga shirin da ta ke yi na maida masu neman mafaka Rwanda.

O'Flaherty ya nuna damuwarsa game da sabuwar dokar da majalisar dokokin Birtaniya ta samar, inda ya yi gargadin cewar hakan na nuna cewar kotun kasar ba tada ikon cewa komai dangani da lamarin.

Firaministan Birtaniya Rishi Sunak.
Firaministan Birtaniya Rishi Sunak. AFP - TOBY MELVILLE

Wannan mataki na zuwa ne dai a dai-dai lokacin da akalla mutane 5 ciki harda karamin yaro suka nutse a ruwa, a kokarin tsallaka ruwa daga Faransa zuwa Birtaniya, lamarin da ya sanya firaministan kasar Rishi Sunak ya ce babu abinda zai hana kasar maida masu neman mafaka Rwanda, don kare asarar rayukan da ake samu.

Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a hadarin da ya faru a wani karamin jirgin ruwa mai dauke da mutane 110, akwai mace daya da yaro daya sai maza 3.

Jami'an tsaron gabar tekun Faransa na ci gaba da aikin neman wadanda suka bace a hadarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.