Isa ga babban shafi

Macron na fatan daukar matakai masu dorewa don habaka samar da makamai

A yau alhamis shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kira da a dauki matakai masu dorewa don kara habaka samar da makamai biyo bayan mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine a lokacin da ya ziyarci wata masana'antar hoda da za a gina nan gaba a garin Bergerac da ke kudu maso yammacin Faransa don magance karancin harsasai da ake fuskanta a wannan yaki na Ukraine.

Shugaba Macron da takwaransa na Ukraine Zelensky a Paris
Shugaba Macron da takwaransa na Ukraine Zelensky a Paris © AP
Talla

Shugaba Macron ya karasa da cewa,babu lokaci a gaban su,nauyi ya rataya wuyan su na ganin sun samar da wadanan kayaki masu inganci cikin gaggawa.

Macron ya na mai jaddada cewa dole ne su yi sauri, banda haka zasu yi aiki tukuru, kasashen su zasu amfana matuka,  yana mai cewa kokarin kuma dole ne ya kasance mai dorewa.

Shugaban Faransa Macron a lokacin da ya ziyarci masana'antar kera makamai a Faransa
Shugaban Faransa Macron a lokacin da ya ziyarci masana'antar kera makamai a Faransa AFP - LUDOVIC MARIN

Eurenco, babbar masana’anta mai samar da hoda da abubuwan fashewa na Turai, za  ta soma aiki a yankin Bergerac a shekarar 2025 kuma za ta samar da tan 1,200 na wannan makamashi a kowace shekara.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta ce masana’antar ta samu umarnin ci gaba da aiki  har zuwa shekarar 2030.

An yi amfani da wannan masa’anta don samar da hoda tan 1915 a lokacin yakin duniya na daya, amma aka rushe masana’antar a cikin 2007 saboda rashin isassun kayan aiki.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a kokarinsa na samar da kayan yaki ga Ukraine
Shugaban Faransa Emmanuel Macron a kokarinsa na samar da kayan yaki ga Ukraine AFP - LEWIS JOLY

Shugaban Eurenco Thierry Francou ya ce yanzu haka sun rugumi fara aiki tukuru,alkawarin da ke zuwa a wani lokaci da Shugaban Faransa ko a watan Yunin shekarar da ta gabata ya bukaci ganin a inganta kasafin kudin tsaro a Turai, yana mai cewa Faransa na kan  turba mai kyau a fanin da ya shafi  inganta tsarin tattalin arziki a bangaren yaki.

A shekarar 2023 ne a ne birnin Paris Shugaban Macron ya shigar da bukatar ganin an samar da kayan aikin soja na Euro biliyan 20, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 21, wanda kashi uku ya fi na shekarun baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.