Macron ya sha alwashin ci gaba da baiwa Ukraine makamai don kare kanta
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya shaidawa takwaran san a Ukraine Volodymyr Zelensky cewar zasu ci gaba da bashi makamai domin kare kasar sa daga mamayar Rasha.
Wallafawa ranar:
Talla
Sanarwar da fadar shugaban Faransa ta gabatar yace kasar na baiwa Ukraine makamai, kuma zata kara yawan su a cikin kwanaki da kuma makwanni masu zuwa tare da kayan jinkai.
Kafin dai wannan lokaci Faransa na jan kafa wajen baiwa Ukraine makamai, saboda rawar da Macron ke takawa na mai sasantawa wajen Magana da shugaban Rasha Vladimir Putin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu