Isa ga babban shafi
Macron - Putin

Putin ya sha alwashin cimma burinsa a Ukraine ko ta halin kaka - Macron

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya shaidawa takwaransa na Faransa Emmanuel Macron cewa Moscow za ta cimma muradanta a Ukraine ko dai ta hanyar yaki ko kuma ta fuskar Diflomasiyya.

Shugaban Rasha Vladimir Poutine da na Faransa Emmanuel Macron yayin wata ganawa a shekarar 2019
Shugaban Rasha Vladimir Poutine da na Faransa Emmanuel Macron yayin wata ganawa a shekarar 2019 © LUDOVIC MARIN / POOL / AFP
Talla

Fadar shugaban Faransa ta Elysee cikin sanarwar da ta fitar game da tattaunawar wayar tarho da shugabannin biyu suka yi ta tsawon sa’a guda da mintuna 45 a ranar lahadi, ta ce shugaba Macron ya roki Putin ya kawo karshen salwantar da rayukan fararen hula, ko da ya ke shugaban na Rasha ya musanta cewa hare-haren sojinsa ke sabbaba asarar rayukan fararen hula.

Acewar Putin kamar yadda fadar Elysee ta sanar, ba ya daga cikin  shirinsa farmakar tashar nukiliyar Ukraine kuma yanzu haka a shirye ya ke ya gana da jami’an hukumar nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya don tattauna yadda za a bai wa tashar kariya.

Yayin zantawar shugaba Putin ya bukaci tabbatar da kasancewar yankin Crimea da Rasha ta kwace a 2014 a matsayin halastaccen yankinta haka zalika ‘yancin yankunan Ukraine din biyu don tabbatar da ballewarsu, bukatun da wani babban jami’in gwamnatin Ukraine da ya nemi a boye sunansa ya ce sam ba masu yiwuwa ba ne.

Acewar fadar Kremlin, yayin zantawar ta jiya wadda ita ce irinta ta 4 da Putin ya yi da Macron tun bayan farowar yakin, shugaban na moscow ya dora laifi kan mahukuntan Ukraine da ya ce sun gaza mutunta yarjejeniyar kwashe fararen hular da aka cimma inda har zuwa suka bar tarin fararen hula a birnin Mariupol mai tsahar jiragen ruwa duk da yadda ya fada hannun sojin Rasha.

Ko a makon jiya shugaba Macron ya gargadi kan barazanar nukiliya a Ukraine bayan farmakin kan tashar Zaporizhzhia mafi girma a nahiyar Turai

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.