Isa ga babban shafi

Macron ya yi alkawarin taimakawa Ukraine da karin makamai

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sha alwashin aikewa da karin makamai da kayan agaji zuwa Ukraine, a wani bangare na kokarin da kasashen duniya ke yi na taimakawa kasar da ke fafata yaki da sojojin Rasha.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. © AFP / LUDOVIC MARIN
Talla

Macron yayi alkawarin kara tallafi ga Ukraine ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar Volodymyr Zelensky a jiya Asabar.

Wasu bayanai sun nuna cewa, tun bayan da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ba da umarnin kaddamar da yaki kan Ukraine a ranar 24 ga Fabrairu, Faransa ta aike da tan 615 na kayayyakin bukata ga kasar da suka hada da na kiwon lafiya, injunan samar da lantarki ga asibitoci, da abinci da kuma motoci.

Kafin yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine, shugaban Faransa yayi ta kokarin shiga tsakani domin sansanta kasahen da ke makwaftaka da juna, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.