Isa ga babban shafi

Ukraine ta kaddamar da shirin bude ofisoshin jakadanci a fadin Afirka

A wani mataki na tunkarar Rasha a fagen siyasa da diflomasiya,Ukraine ta bude ofishin jakadancinta a Cote D’Ivoire a yau Alhamis, kwana guda bayan bude ofishin jakadanci a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, a daidai lokacin da Kyiv ke neman karin girma a Afirka don dakile tasirin Moscow.

Shugaban Ukraine
Shugaban Ukraine via REUTERS - Handout .
Talla

 

Ministan harkokin wajen kasar Ukraine Maksym Subkh a lokacin gabatar da jawabi,ya ne mai cewa an shiga sabuwar tafiya a cikin sabon tarihin dangantakar dake tsakanin Ukraine da wasu kasashen Afirka kama daga Cote D’Ivoire da wasu kasashen na nahiyar.

Sabbin ofisoshin jakadancin sun kasance sakamakon "umarnin shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky na yada huldar diflomasiyyar Ukraine a Afirka", in ji shi.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a fagen yaki
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a fagen yaki AP

Subkh ya bude ofishin jakadancin Kyiv a Kinshasa a ranar Laraba a daidai lokacin da ake shirin bude wasu ofishoshin da dama a Afirka don karfafa tallafi, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta shaida wa kamfanin dilancin labaren Faransa na AFP.

Kasashe aminan kasar Ukraine
Kasashe aminan kasar Ukraine © Piroschka Van De Wouw / Reuters

Ministan harkokin wajen kasar Ukraine Maksym Subkh zai kai ziyara kasashen Ghana, Mozambique, Botswana da Rwanda domin kaddamar da ofisoshin jakadanci a makonni masu zuwa, kamar yadda wakilin sabon ofishin jakadancin a Abidjan ya tabbatar.

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky AFP - MANDEL NGAN

Ministan harkokin wajen kasar Ukraine Maksym Subkh ya kuma godewa hukumomin Cote D’Ivoire ganin goyon bayan da suka bayar  a wannan yaki da Ukraine ke yi da Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.