Isa ga babban shafi

Birtaniya za ta fara biyan bakin haure fan dubu 3 don tisa keyarsu zuwa Rwanda

Birtaniya za ta fara biyan mutanen da suka rasa damar samun mafaka a cikin kasar tsabar kudi fam dubu 3 dai dai da dalar Amurka dubu 3 da 800 don tisa keyarsu zuwa Rwanda amma bisa radin kansu.

Bakin da ke neman mafaka a kasashen Turai.
Bakin da ke neman mafaka a kasashen Turai. AP - Jussi Nukari
Talla

Tun gabanin wannan mataki Birtaniya na amfani da wani tsarin biyan masu neman mafakar wasu kudade don mayar da su kasashensu na asali, tsarin da shi kansa ke gamuwa da kakkausar suka ‘yan fafutukar kare hakki.

Sai dai majiyoyi sun ce wannan sabon tsarin zai shafi masu neman mafakar da suka rasa damar zama a Birtaniya kuma ba za su iya komawa kasashensu na asali ba.

Shirin biyan kudaden don tisa keyar masu neman mafakar zuwa Rwanda da Firaminista Rishi Sunak ya gabatar wani yunkuri ne zaftare yawan bakin hauren da ke kwarara cikin Birtaniya.

Haka zalika matakin na zuwa ne bayan Majalisar dattijan Birtaniya ta yi watsi da kudirin Birtaniya na girke bakin da ke neman mafaka a Birtaniyar can a Rwanda bayan tun farko kotu ta bayyana kasar a matsayin mafi cikakken tsaron da za ta bayar da kariya ga tarin bakin hauren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.