Isa ga babban shafi

Yawaitar kai wa dalibai hari ya tayar da hankalin mahukuntan Faransa

Wani dalibi mai kimanin shekaru 15  ya rasa ransa a Faransa sakamakon raunukan da ya samu, bayan dukan kawo wukan da wasu suka lakada masa.

kofar makarantar Les Sablons inda aka lakadawa wani dalibi dukan kawo wuka da ya kai ga mutuwarsa a Faransa.
kofar makarantar Les Sablons inda aka lakadawa wani dalibi dukan kawo wuka da ya kai ga mutuwarsa a Faransa. © Miguel Medina, AFP
Talla

Bayanai sun ce a ranar Alhamis din da ta gabata ne gungun wasu matasa suka yi masa rubdugun a kusa da makarantarsa da ke kudancin birnin Paris, lamarin da ya janyo masa bugun zuciya, wanda kuma bayan garzayawa da shi asibiti ya mutu a ranar Juma’a.

Karo na biyu kenan cikin mako guda da aka aikata irin wannan cin zali a Faransa, inda a ranar Talata, wata daliba mai shekaru 13 ta shiga dogon suma bayan dukan da wasu suka lakada mata a harabar makarantar da take zuwa a birnin Montpellier.

Wadannan lamurra na zuwa ne a yayin da hankalin mahukuntan Faransa ya tashi biyo bayan yawaitar sakwannin barazanar kai wa matsa hari da ake aikewa da su a makarantu da dama.

Domin shawo matsalar ce ma, shugaban Emmanuel Macron ya ce dole a dauki matakan bai wa makarantun kasar kariya daga wannan barazana.

A nata bangaren, rundunar ‘yan sandan Faransa ta sanar da kama wani matashi mai shekaru 17, bisa tuhumarsa da hannu a mutuwar dalibin baya bayan nan da aka kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.