Isa ga babban shafi

Faransa ta ce 'har yanzu' juyin mulkin Nijar bai tabbata ba

Faransa, ta ce har yanzu ba ta da yakinin cewa juyin mulkin da wasu sojoji ke cewa sun yi wa gwamnatin dimokuradiyya ta Jamhuriyar Nijar ya kai ga samun nasarar. Wadanann dai kalamai ne da suka fito daga bakin ministar harkokin wajen kasar Catherine Colonna, a daidai lolkacin da babban kwamandan askarawan kasar ta Nijar Janar Sidikou Abdou Issa ke cewa shi ma yana goyon bayan masu juyin mulkin. 

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugaba Mohamed Bazoum a Faransa ranar 16 ga watan Fabrairu 2023.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugaba Mohamed Bazoum a Faransa ranar 16 ga watan Fabrairu 2023. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

A cewarministaCatherine Colonna, lura da yaddalamurrakegudana a wannanlokaci, Faransaba ta ganincewajuyinmulkin bai tabbataba, inda ta ce yanzuhakakungiyarkasashenYammacinAfirkaEcowas/Cedeao na shiringudanar da tarongaggawadangane da halin da akeciki a Nijarwatakila a ranarlahadi mai zuwa. 

Kanal-Manjo Amadou Abdramane yayin gabatar da jawabin a gidan talibijin din kasar, bayan hambarar da shugaba Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin 2023.
Kanal-Manjo Amadou Abdramane yayin gabatar da jawabin a gidan talibijin din kasar, bayan hambarar da shugaba Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin 2023. AP

Wannan na zuwa ne a daidailokacin da fadar shugabanFaransakecewaanzantatawayartarhotsakanin Mohamed Bazoum da kuma Emmanuel Macron, yayinda a nasubangaresojojin da keikirarinkwacemulkikezarginFaransa da karyadoka, tahanyarsauka da wanijirginsoji  a safiyarjiyaalhamis a Yamai, duk da cewaiyakokinkasar na rufe. 

Masu zanga-zanga nuna goyan baya ga juyin mulkin Nijar
Masu zanga-zanga nuna goyan baya ga juyin mulkin Nijar AFP - -

BabbanMagatakarda na MDD Antonio Guterres yayikashedi a game da illolin da wannanlamari na Nijarzaiiyayiwayankin Sahel, wandake fama da matsalolintsaro, karancinabinci da kumarashindimokuradiyya a Mali, Burkina Faso da kumaChadi. 

Bayanwatatattaunawatawayartarho da tayui da Mohamed Bazoum, jakadiyarAmurka a MDD Linda Thomas-Greenfield a jiyaalhamis, Amurkanta sanar da cewa tana goyonbayandukwasumatakai da KwamitinTsarozaidaukadominkwantar da hankula a Nijar. 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.