Isa ga babban shafi

Shugaba Macron na Faransa ya yi tir da shigowar mulkin mallaka a yankin Pacific

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi gargadi game da sabuwar daular mulkin mallaka a yankin tekun Pasifik yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai yankin, inda ya yi tir da dabi'ar kaka-gida da manyan kasashe ke yi a yankin wato inda kasar China ke kara karfafa huldar kasuwanci da tsaro.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gabatar da jawabi a yayin bikin cika shekaru 140 da kafa cibiyoyin kawancen Faransa a fadar shugaban kasa ta Elysee da ke birnin Paris na Faransa a ranar 21 ga Yuli, 2023.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gabatar da jawabi a yayin bikin cika shekaru 140 da kafa cibiyoyin kawancen Faransa a fadar shugaban kasa ta Elysee da ke birnin Paris na Faransa a ranar 21 ga Yuli, 2023. via REUTERS - POOL
Talla

Faransa wacce ke da tsibiran da suka mamaye yankin Indo-Pacific da suka hada da Polynesia ta Faransa, ta kara karfafa huldar tsaro da Indiya da sauran kasashen yankin a wani mataki na dakile tasirin China.

A wani jawabi da ya yi a Vanuatu, Macron, shugaban Faransa na farko da ya taka kafarsa a tsibirin Pacific tun bayan Charles de Gaulle, ya ce Faransa za ta yi aiki kafada da kafada da kasashen yankin don kare 'yancin kansu.

Kasashen tsibiran Pasifik na neman kasar China, wadda ta kasance babbar mai ba da rance domin gina ababen more rayuwa yayin da ta kulla yarjejeniyar tsaro da tsibiran Solomon a bara, da kuma Amurka da ke sake bude ofisoshin jakadancinta da aka rufe tun bayan yakin cacar baka.

Kasar China ta kasance babbar mai ba da rancen ababen more rayuwa ga kasashen tsibiran Pacific ciki har da Vanuatu cikin shekaru goma da suka gabata, domin kuwa babban mai ba da lamuni na Vanuatu shi ne bankin EXIM na kasar China wanda ke da kashi uku na bashin kasar, a cewar asusun lamuni na duniya IMF.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.