Isa ga babban shafi

Dakarun da suka tsare shugaba Bazoum sun tarwatsa 'yan kasar da harbi

Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da Kungiyar Kasashen Turai EU da Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS sun yi Allah-wadai da abin da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar, inda wasu dakaru da ke tsaron fadar shugaban kasa suka tsare shugaba Mohammed Bazoum a wani yunkuri na juyin mulki, yayin da 'yan kasar suka fara gudanar da zanga-zanga.

Shugaban Nijar Mohamed Bazoum.
Shugaban Nijar Mohamed Bazoum. © RFI/France 24
Talla

Masu goyon bayan Bazoum ne suka doshi fadar shugaban kasar, amma dakarun da suka yi garkuwa da shi suka tarwatsa su da harbin bindiga.

Wasu daga cikin magoya bayan shugaban Nijar, Mohamed Bazoum da ke zanga-zangar adawa da yunkurin yi masa juyin mulki.
Wasu daga cikin magoya bayan shugaban Nijar, Mohamed Bazoum da ke zanga-zangar adawa da yunkurin yi masa juyin mulki. AFP - -

A cikin kakkausar lafazi, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres ya caccaki yunkurin juyin mulkin da ya bayyana a matsayin zagon-kasa ga gwamnatin demokuradiya da kuma sukurkuta zaman lafiyar kasar.

Guterres ya yi kira ga dukkanin masu hannu a wannan yunkurin na juyin mulki da su janye matakinsu domin kare dokokin kundin tsarin mulki.

Ita ma fadar White ta shugaban Amurka ta ce tana cikin damuwa kan abin da ke faruwa a Nijar, inda ta yi tur da tsare shugaba Bazoum tare da jan kunnen dakarun suka tsare shi da su gaggauta sakin sa domin kauce wa tashin hankali a kasar.

Haka nan Kungiyar Kasashen Turai ta EU ta bakin shugaban kula da manufofinta na ketare, Josep Borrell ta caccaki abin da ta kira yunkurin wargaza demokuradiya da kuma barazana ga zaman lafiyar Nijar.

Tuni Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS ta nada shugaban Benin, Patrice Talon domin jagorantar wata tawaga ta musamman da aka kafa domin shiga tsakanin bangarorin biyu da zummar sasanta rikicin na juyin mulki.

Wannan hoton da aka dauka a ranar 22 ga watan Afrilun shekarar 1974 a birnin Yamai na dauke laftanar kanar Seyni Kountché jim kadan da juyin mulkin da ya yi wa Hamani Diori.
Wannan hoton da aka dauka a ranar 22 ga watan Afrilun shekarar 1974 a birnin Yamai na dauke laftanar kanar Seyni Kountché jim kadan da juyin mulkin da ya yi wa Hamani Diori. © AFP

ECOWAS ta nanata cewa, ba za ta lamunci ci gaba da samun juye-juyen mulki ba a kasashen Afrika ta yamma.

Shugaba Bazoum wanda amini ne na kut da kut da Faransa, an zabe shi ne a shekarar 2021 domin jagorantar kasar da ke fama da talauci, yayin da take da tarihin samun rashin zaman lafiya.

Nijar ta gamu da juye-juyen mulki har sau hudu tun bayan karbar 'yancinta daga Faransa a shekarar 1960 baya ga dimbin yunkuri iri-iri da aka yi na kifar da wasu shugabannin kasar daga kan karaga.

Tun daga shekarar 2020, an samu akalla juyin mulki har sau biyar a wasu kasashen yammacin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.