Isa ga babban shafi

Sojojin Nijar ba su da hurumin korar jakadan Faransa- Macron

A wani jawabi da ya gabatar da safiyar yau Litinin, shugaba Emmanuel Macron ya bayyana cewa sojojin da ke mulkin Nijar ba su da hurumin korar jakadan kasar Sylvain Itte wanda mahukuntan na Yamai suka bai wa wa'adin sa'o'i 48 ya fice daga kasar.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa yayin jawabin da ya gabatar a safiyar yau litinin.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa yayin jawabin da ya gabatar a safiyar yau litinin. via REUTERS - POOL
Talla

Tun gabanin jawabin na Macron, bayanai sun ce jakadan na Faransa Sylvain Itte ya ci gaba da kasancewa a birnin Yamai duk kuwa da yadda dubun dubatar al’ummar kasar suka gudanar da wata zanga-zangar bukatar gaggauta ficewarsa daga kasar bayan cikar wa'adin da aka dibar masa na sa'o'i 48.

Masu zanga-zangar sun yi dandazo a gab da sansanin sojin Faransar da ke birnin Yamai, wasunsu na rike da tutar Nijar yayin da wasu ke daga tutar Rasha, a bangare guda kuma wasu ke daga allunan masu rubutun bukatar ficewar dakarun Faransa daga kasar.

Faransa wadda ita ta yi wa Nijar mulkin mallaka, har yanzu tana da dakaru dubu 1 da 500 wadanda ke aikin taimaka wa tsohuwar gwamnatin Mohamed Bazoum yaki da matsalar tsaron da ta dabaibaye kasar gabanin hambarar da shi a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.

Tun da sanyin safiyar jiya Lahadi aka faro zanga-zangar wadda dubban mutane suka yi kawanya ga sansanin sojin saman kasar wanda a nan ne dakarun Faransa suke.

Wani bangare na masu zanga-zangar nuna goyon baya ga mulkin sojin Nijar a ranar Lahadi.
Wani bangare na masu zanga-zangar nuna goyon baya ga mulkin sojin Nijar a ranar Lahadi. REUTERS - STRINGER

Galibin masu zanga-zangar sun rika rera waken ‘‘Ba ma bukatar sojojin Faransa a kasarmu’’ wasu kuma na fadin ‘‘Faransawa su fice’’.

Zanga-zangar na zuwa ne bayan shafe wata guda ana takun-saka tsakanin Faransar da Nijar biyo bayan juyin mulkin, inda a Juma’ar da ta gabata Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar ta bai wa jakadan Faransa a kasar Sylvain Itte wa’adin sa’o’i 48 kan ya gaggauta ficewa.

Sojojin da ke mulki a Nijar sun zargi jakadan da kin mutunta sabbin dokokin da suka gindaya, kodayake tuni Faransa ta yi watsi da wannan umarni bisa kafa hujja da cewa sojojin ba su da hurumin tisa keyar jakadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.