Isa ga babban shafi

Sojojin Nijar na ganawa kan janyewar Faransa daga kasar

Firaministan da sojoji suka nada a Jamhuriyar Nijar, Ali Mahaman Lamine Zeine ya ce suna ci gaba da tatatunawa da zummar ganin sojojin Faransa sun fice daga cikin kasar, yayin da ya jaddada cewar za su ci gaba da alaka da kasar da ta yi musu mulkin mallaka. 

Prime ministan na Nijar ya ce lokaci yayi da ya kamata sojojin Faransa su  bar kasar
Prime ministan na Nijar ya ce lokaci yayi da ya kamata sojojin Faransa su bar kasar AFP - KAREN BLEIER
Talla

Zeine ya shaida wa manema labarai a birnin Yamai cewar, sojojin Faransa na zama ne a haramtaccen wuri, saboda haka yanzu ake tattaunawa domin ganin sun janye cikin gaggawa. 

Firaministan ya bayyana cewar suna bukatar ci gaba da hulda da Faransa, kasar da suke da alaka mai girma a tsakaninsu. 

Takun-saka tsakanin Nijar da Faransa ya yi tsanani tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa shugaba Bazoum Mohammed a ranar 26 ga watan Yuli, abin da Faransar ta ce ba za ta amince da shi ba. 

Yanzu haka sojojin Faransa 1,500 ke zama a cikin Nijar domin yaki da ‘yan ta’adda a yankin Sahel, sakamakon yarjejeniyar sojin da kasashen biyu suka kulla a tsakaninsu. 

A ranar 3 ga watan Agusta, sojojin da suka yi juyin mulkin suka sanar da bijire wa yarjeniyoyin da suka kulla da kasar. 

Daya daga cikin yarjeniyoyin ta bada damar bai wa wa’adin wata guda na janye sojojin. 

Har ila yau Nijar ta janye takardar zaman jakadan Faransa Sylvain Itte a Yamai, inda ta bukaci ficewarsa daga kasar, yayin da gwamnatin Faransa ta sa kafa ta shure bukatar saboda rashin amincewa da sojojin da ke mulkin. 

Firaministan Nijar lamine Zein ya  ce jakadan na Faransa ya saba wa dokokin kasar wajen kin amsa gayyatar da hukumomin Nijar suka yi masa ranar 25 ga watan Agusta. 

A karshen makon da ya gabata, dubun-dubatar mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Yamai domin neman ganin sojojin Faransar sun fice daga kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.