Nijar ta kori jakadunta dake Amurka da Faransa da Togo da kuma Najeriya
Shugabannin juyin mulki a jamhuriyar Nijar sun sanar da kawo karshen wa’adin ayyukan jakadun su a wasu kasashe hudu a kasar da yammacin ranar Alhamis yayin da suke fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya na maido da zababben shugaban da suka hambarar a makon jiya.
Wallafawa ranar:
A cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar, sun dakatar da ayyukan manyan jakadun kasashen Faranasa da Amurka da Najeriya da kuma Togo da Jamhuriyar Nijar.
Majalisar mulkin sojan dai na fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya na ganin ta maido da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum, inda kungiyar kasashen yammacin Afirka, karkashin jagorancin shugaban Najeriya Bola Tinubu ta yi barazanar yin amfani da karfin tuwo don kwato mulki.
Martani
Rundunar sojan ta kuma yi barazanar mayar da martani nan take ga duk wani "yunkuri na zalunci kan gwamnatinsu."
Yayin da makwabtanta Maji da Burkina Faso suka yi gargadi kan daukar duk wani mataki na soja a kan Nijar, wanda suka ce zai daidai da shelanta yaki a kansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu