Isa ga babban shafi
Labarin RFI Hausa

Tsohon shugaban Najeriya zai jagoranci ganawar ECOWAS da sojojin Nijar

Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma, wato ECOWAS ta nada tsohon shugaban Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar a matsayin shugaban tawagar da za ta je Nijar gobe laraba domin ganawa da sojojin da suka yi juyin mulki. 

Tsohon shugaban Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar
Tsohon shugaban Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar © Daily Trust
Talla

 

Wata majiya daga Cibiyar ECOWAS ko kuma CEDEAO dake Abuja tace daga cikin wadanda zasu shiga tawagar harda Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar. 

Wannan itace zata zama tawaga ta farko daga ECOWAS da zata gana da sojojin baya ga ziyarar da shugaban kasar Chadi Janar Mahamat Idriss Deby ya kai inda ya gana da shugaban sojin da suka yi juyin mulki, Janar Abderahmane Tchiani da shugaba Bazoum Mohammed da kuma tsohon shugaban kasda Mahamadou Issofou. 

Ana saran tawagar ta gabatarwa sabbin shugabannin sojin Nijar matsayin ECOWAS dangane da juyin mulkin da kuma jin ta bakin su dangane da sakon da zasu bayar. 

Shugabannin kasashen ECOWAS sun bayyana rashin amincewar su da juyin mulkin da ya kawar da shugaba Bazoum Mohammed daga karagar mulki, tare da gudanar da taron gaggawa a karshen mako domin daukar matsayin bai daya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.