Isa ga babban shafi

Burkina da Mali sun ce za su mayar da martani idan ECOWAS ta kai wa Nijar hari

Kasashen Mali da Burkina Faso sun gargadi kungiyar kasashen yammacin Africa ta ECOWAS/CEDEAO game da yunkurin amfani da sojoji wajen murkushe sojojin da suka yi juyin Mulki a Nijar. 

 Ibrahima Traoré shugaban mulkin sojin Burkina Faso.
Ibrahima Traoré shugaban mulkin sojin Burkina Faso. © Kilaye Bationo / AP
Talla

Ta cikin wata sanarwar hadin gwiwa da sojojin na Mali suka karanta ta kafar Talabijin din kasar, sun ce za su dauki duk wani harin soja kan Nijar a matsayin kaddamar da yaki a kan su, kuma babu makawa zasu mayar da martani. 

Sanarwar sojojin ta kuma kara da cewa matukar ECOWAS ta yi gangancin afkawa sojojin Nijar, tabbas zasu fice daga kungiyar kuma zasu marawa takwarorin su na Nijar baya, wajen mayarwa da ECOWAS martanin sojin.  

Sanarwar sojojin na zuwa ne dai-dai lokacin da kasashen duniya ke barzanar afkawa sojojin na Nijar matukar basu mayar da Mulki hannun farar hula ba. 

Najeriya da ke makociyar Nijar ta kusa, kuma jagorar ECOWAS ta sanar da cewa ta shirya tsaf wajen fadawa Nijar da zarar sojojin ta sun sami umarnin hakan 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.