Isa ga babban shafi

Dalilin da ya sa ECOWAS ke bukatar rundunar kai daukin gaggawa

Gwamnatin Najeriya ta ce kungiyar kasashen Afirka ta Yamma, wato ECOWAS na bukatar rundunar soji ta din-din-din wadda za ta dinga kai dauki a kasashen dake yankin idan bukatar haka ta taso. 

Tutar kungiyar kasashen yankin yammacin Afirka ta ECOWAS/CEDEAO
Tutar kungiyar kasashen yankin yammacin Afirka ta ECOWAS/CEDEAO REUTERS - FRANCIS KOKOROKO
Talla

 

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana bukatar samar da wannan rundunar domin taimakawa yankin kawar da juyin mulkin soji da kuma murkushe wasu matsalolin tsaron da suka addabi yankin, bayan nadin da aka masa na jagorancin shugabannin kasashen dake yankiin. 

Mai magana da yawun Tinubu, Dele Alake yace rashin samun wannan runduna a kasa ta taimaka wajen kasa warware matsalar da aka samu jiya a Nijar, inda dakarun fadar shugaban kasa suka yi garkuwa da shugaba Bazoum Mohammed na dogon lokaci, ba tare da an kai masa dauki ba. 

Alake yace tun bayan samun labarin abinda ke faruwa a Nijar, shugaba Tinubu ke ta tintibar abokan aikinsa, sauran shugabannin yankin da kuma masu karfin fada aji akan irin matakan da ya dace a dauka domin shawo kan matsalar ta Nijar, tare da gabatar da sanarwa ta musamman a matsayin shugaban ECOWAS wanda ya yi Allah wadai da halin da ake ciki a Nijar. 

Mai magana da yawun gwamnatin yace wannan ya Tinubu nada shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon a matsayin jakada domin tafiya Nijar dan ganawa da bangarorin sojin da suka yi garkuwa da Bazoum da kuma hana sojojin dake goyan bayan shugaban afkawa fadar shugaban kasda. 

Alake ya bayyana Bazoum a matsayin daya daga cikin shugabannin ECOWAS dake matukar adawa da mulkin soji, kamar yadda ya nuna a taron shugabannin ECOWAS da aka yi a Guinea Bissau, ashe sojojin s ana kitsa shirin hambarar da shi ba tare da ya sani ba. 

Mai magana da yawun Tinubu yace ECOWAS na ci gaba da tintiba da kuma bin matakan da suka dace wajen ganin na kawo karshen wannan matsala ta Nijar cikin sauri da kuma tabbatar da dorewar dimokiradiyar kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.