Isa ga babban shafi

ECOWAS ta mayar da martani kan fargabar yunkurin juyin mulki a Nijar

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu wanda a yanzu haka yake jagorancin kungiyar hadin kan kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ya ce ba za su lamunci duk wani mataki da zai haifar da nakasu ga halastaciyyar gwamnatin Jamhuriyar Nijar ba.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kuma sabon shugaban kungiyar ECOWAS.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kuma sabon shugaban kungiyar ECOWAS. © Twitter/DOlusegun
Talla

 

Gargadin na Bola Tinubu na kunshe ne cikin sanarwar da ya fitar a matsayinsa na shugaban kungiyar ECOWAS domin mayar da martani kan fargabar yunkurin juyin mulkin da aka yi a Nijar da safiyar wannan Laraba.

Shugaban Najeriyar ya ce shi da sauran takwarorinsa na yammacin Afirka na bibiyar abin da ke wakana sau da kafa a Jamhuriyar Nijar, kuma za su dauki dukkanin matakan da suka dace wajen hana rusa zababbiyar gwamnatin kasar.

Tinubu ya kara da cewar zai ci gaba da ganawa da sauran shugabannin yammacin Afirka tare da shan alwashin kare mulkin dimokaradiya tare da mutunta kundin tsarin mulkin da ta kunsa.

Wannan matsala ta Nijar na zuwa ne a daidai lokacin da sabon shugaban ECOWAS Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin kawo karshen juyin mulki a yankin Afirka ta Yamma.

Ko a makon jiya sai da Tinubu ya jagoranci wani kwaryakwaryan taro a Abuja wanda ya kunshi shugaban Nijar Bazoum Mohamed da na Guinea Bissau Oumar Sissoko Embalo, da na Jamhuriyar Benin Patrice Talon akan yadda za a tuntubi shugabannin sojin Mali da Guinea da Burkina Faso domin ganin sun mayar da gwamnatocin fararen hula karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.