An kama sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki a Nijar
An kama wasu sojoji bayan sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar a sanyiin safiyar Larabar nan, yayin da aka dauki tsawon lokaci ana harbe-harben bindiga a babban birnin Yamai.
Wallafawa ranar:
Mazauna birnin sun ce, sun kwashe tsawon dare suna jin karar harbe-harben bindiga a kusa da fadar shugaban kasar , al’amarin da ke zuwa a daidai lokacin da ya rage kwanaki biyu a rantsar da Bazoum Mohamed a matsayin sabon shugaban kasar.
Mazauna birnin sun ce, da misalin karfe uku na dare aka yi ta harbe-harbe da manya da kananan makamai, inda aka dauki tsawon minti 20 ana bude wuta.
Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce, tuni aka cafke sojojin da ake zargi da kitsa juyin mulkin da bai yi nasara ba.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Mohamane Ousmane ke ci gaba da ikirarin cewa, shi ya lashe zaben shugaban kasar zagaye na biyu da aka gudanar a ranar 2 ga watan jiya duk da cewa Kotun Fasalta Kundin Tsarin Mulki ta tabbatar da nasarar Bazoum.
Ousmane ya bukaci magoya bayansa da su gudanar da tattaki cikin lumana a sassan kasar, amma hukumomin Nijar sun haramta gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati a ranar Laraba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu