Isa ga babban shafi

Muna kan bakammu na kawo karshen juyin mulki a Afirka - ECOWAS

Shugabannin kasashen ECOWAS sun sake bayyana aniyarsu ta ganin an murkushe duk wani yunkuri na juyin mulki a yankin, domin tabbatar da mulkin dimokiradiya da kuma baiwa jama’a damar zabin shugabancin da suke so. 

Shugabannin ECOWAS yayin taron da ya gudana a Abuja
Shugabannin ECOWAS yayin taron da ya gudana a Abuja © ECOWAS
Talla

Shugabannin sun bayyana haka ne bayan wani kwarya kwaryan taron da suka yi a Abuja, wanda ya samu halartar shugabannin kasashen Najeriya da Nijar da Guinea Bissau da Jamhuriyar Benin da kuma shugaban gudanarwar kungiyar, Omar Alieu Touray. 

Shugabannin sun bayyana sanya shugaba Patrice Talon na Benin a matsayin wanda zai tintibe sojojin dake mulki a nahiyar da zummar gabatar da shirin su na gudanar da zabe wanda zai mayar da mulkin dimokiradiya a kasashen su. 

Taron shugabannin na rana guda ya kuma bayyana shirin ECOWAS na maye gurbin sojojin Majalisar Dinkin Duniya da suka fice a Mali da sojojin da zasu fito daga kasashen ECOWAS. 

Idan ba’a manta ba, Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana shirin janye dakarun ta daga Mali kamar yadda hukumomin kasar suka bukata, bayan ficewar sojojin Faransa dake taimaka musu wajen yaki da ‘yan ta’adda. 

Kasar Mali na daga cikin kasashen da ke karkashin mulkin soji, baya ga Guinea da Burkina Faso. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.