Isa ga babban shafi
ECOWAS

Shugabannin ECOWAS sun gana kan kasashen Mali da Guinea

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin wasu shugabannin kasashen yammacin Afrika da suka halarci taron kungiyar ECOWAS karo na 60.

Taron ECOWAS.
Taron ECOWAS. © REUTERS - KWEKU OBENG
Talla

Yayin taron wanda aka fara da safiyar Lahadin nan, shugabannin ECOWAS sun tattauna kan muhimman batutuwan da dama, ciki har da rahotanni akan rikicin siyasa a Mali da kuma Guinea Conakry.

Daga cikin shugabannin da suka samu halartar taron  a Abuja, akwai shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ta ECOWAS, tare da shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe Eyadema, da shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohamed.

Goodluck Jonathan, tsohon shugaban Najeriya kuma jakadan da ECOWAS  ta tura Mali a matsayin babban mai shiga tsakanin rikicin siyasar kasar ma ya halarci taron na Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.