Isa ga babban shafi
MALI-GUINEA

ECOWAS ta sanyawa shugabannin sojin Mali da Guinea takunkumi

Kungiyar ECOWAS ta sanya takunkumi akan wasu fitattun mutanen dake kasashen Mali da Guinea saboda abinda ta kira rawar da suke takawa wajen jinkirin mayar da kasashen biyu turbar dimokiradiya.

Shugabannin ECOWAS a Ghana
Shugabannin ECOWAS a Ghana © Nigeria presidency
Talla

Shugaban gudanarwar kungiyar Jean-Claude Kassi Brou ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP bayan kammala taron shugabannin da ya gudana a Accra cewar, sun yanke hukunci sanya takunkumi akan wadanda ake zargin suna da hannu wajen samun jikirin.

Brou yace sojojin Mali sun rubutawa shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo dake jagorancin kungiyar cewar ba zasu iya gudanar da zaben shugaban kasa kamar yadda suka yi alkawari ba.

Shugaban mulkin sojin Mali Assimi Goita
Shugaban mulkin sojin Mali Assimi Goita AP

Takunkumin da aka amince da su sun hada da hana tafiye tafiye da kuma rufe asusun ajiyar kudaden wadanda ake zargi tare da iyalan su domin ganin sun sauya matsayin su na yiwa shirin zaben zagon kasa.

Shugabannin kasashen dake ECOWAS sun bayyana rashin gamsuwar su da rashin ci gaban da ake samu wajen shirya zaben shugaban kasar Mali, abinda ya sa wakilan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zuwa kasar.

Wakilan kwamitin sun sake jaddada matsayin su na ganin gwamnatin rikon kwaryar Mali ta mika mulki ga zababbiyar gwamnatin farar hula kamar yadda aka tsara.

Kanar Mamady Doumbouya shugaban mulkin sojin Guinea
Kanar Mamady Doumbouya shugaban mulkin sojin Guinea JOHN WESSELS AFP/File

A ranar 26 ga watan Oktoba, gwamnatin mulkin sojin Mali ta kori Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman dake kasar Hamidou Boly, matakin da ECOWAS tayi Allah wadai da shi.

Taron shugabannin ECOWAS na karshen mako ya kuma amince da ci gaba da dakatar da Guinea daga cikin kungiyar tare da sanya takunkumi akan shugabannin sojin dake mulki tare da iyalan su.

ECOWAS ta bukaci sakin shugaba Alpha Conde daga tsare shi da akayi a gidan sa dake Conakry ba tare da gindaya sharidodi ba, yayin da ta yaba da nada Firaminista farar hula da kuma bukatar gabatar mata da shirin mayar da kasar turbar dimokiradiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.