Kotun ECOWAS/CEDEAO ta dakatar da Mali da Guinea
Kotun Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta dakatar da duk wani shari'ar da ta shafi kasashen Mali da Guinea, kasashen mambobinta biyu da yanzu haka ke karkashin jagorancin sojoji.
Wallafawa ranar:
A cikin wata takarda mai kwanan wata 30 ga watan Satumba, wanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya samu, magatakardar kotun kasashen 16, Tony Anene-Maidoh, ya yi bayanin wannan shawarar, yace matakin na kunshe cikin kundin tsarin Kotun na 78.
Babban magatakardar ya ce daga yanzu "kotun baza tayi aiki da wadannan kasashe biyu ba, har sai lokacin da suka dawo da mulkin farar hula.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu