Isa ga babban shafi

Kotun ECOWAS ta umurci Najeriya ta biya wasu sojoji 244 hakkokinsu

Kotun Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta umurci gwamnatin Najeriya da ta biya wasu sojojin kasar 244 da ta kora daga aiki a shekarar 2016 hakkokin su cikin gaggawa, bayan rundunar sojin kasar ta same su da laifin tserewa daga bakin daga a yakin da suke fafatawa da kungiyar Boko Haram.

Sojojin Ecowas lokacin da suke aiki na musamman a kasar Gambia.
Sojojin Ecowas lokacin da suke aiki na musamman a kasar Gambia. REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

A hukuncin da ta yanke, kotun ta hannu mai shari’a Keikura Bangura, tace korar sojojin daga bakin aiki ya saba ka’ida, saboda haka ta bukaci gwamnatin Najeriya ta biya su hakkokin su, duk da yake kotun taki amincewa da bukatar mayar da su bakin aiki da suka nemi tayi.

Kotun ECOWAS tace gabatar da korar sojojin daga aiki ba tare da gabatar su a gaban shari’a ba domin yi musu hukunci ya saba ka’ida, saboda haka ta bukaci gwamnati ta biya su kudaden su.

Alkalai 3 suka saurari karar suka kuma yanke hukunci, cikin su harda Gberi-Be Ouattara da ya jagoranci shari’ar da Dupe Atoki da kuma Keikura Bangura.

Ita dai rundunar sojin Najeriya tace ta dauki matakin korar sojojin ne saboda tserewa daga bakin daga lokacin da suke fafatawa da mayakan Boko Haram, yayin da sojojin ke cewa gwamnati bata basu cikakkun kayan aikin da zasu fuskanci mayakan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.