ECOWAS na taro a Ghana akan makomar juyin mulkin Mali da Guinea
Shugabanin kasashen ECOWAS za su gudanar da wani taro na musaman dangane da makomar kasashen Guinee da Mali wadanda sojoji suka yi juyin mulki wajen kifar da gwamnatocin fararen hula a cikin su.
Wallafawa ranar:
Ana kyautata zaton Shugabanin za su fi mayar da hankali a hanyoyin da ya dace su bi wajen saka takunkunmi karya tattalin arziki zuwa jami’an dake rike da madafan ikon wadanan kasashe.
Tuni kungiyar ECOWAS ta dakatar da wadannan kasashe daga cikin ta tare da gabatar da bukatar shirya zabe domin mayar da mulki ga fararen hula.
Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Johnatan mai rike da mukamin manzon kungiyar ECOWAS ya gana da shugabanin majalisar sojojin dake rike da mulki a kasashen Mali da Guinee ba tare da cimma matsaya dake tabbatar cewa sojojin na shirye don yin aiki da shawarwarin kungiyar Ecowas da za ta kai su ga shirya zabuka ba kamar yadda aka bukata.
Ita ma kungiyar Afirka ta AU ta bi sahun ECOWAS wajen dakatar da wadannan kasashe daga cikin ta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu