Isa ga babban shafi
Guinea - Juyin mulki

Tawagar ECOWAS ta isa Guinea don ganawa da jagororin juyin mulki

Tawagar kungiyar ECOWAS ta kasashen yammacin Afirka ta isa Guinea domin tattaunawa da shugabannin sojojin kasar da suka yi juyin mulkin da ya kawo karshen gwamnatin tsohon shugaba Alpha Conde.

Taswirar Conakry babban birnin kasar Guinea.
Taswirar Conakry babban birnin kasar Guinea. AFP
Talla

A yayin ziyarar ta ta, tawagar ta ECOWAS za ta bukaci maida mulki ga farar hula a kasar ta Guinea da kuma matsa kaimi kan bukatar gaggauta sakin tsohon shugaba Conde, wanda a yanzu ke tsare a hannun sojoji, tun bayan juyin mulkin da suka yi masa a karkashin jagorancin Laftanar Kanal Mamady Doumbouya ranar Lahadi.

Sannu a hankali dai rayuwa a babban birnin kasar Conakry ta koma daidai a ranar Alhamis, inda aka sake bude kasuwanni, tare da ci gaban harkokin yau da kullum.

Laftanar Kanal Doumbouya na ci gaba da nanata  cewa ya dauki matakin juyin mulki ne domin maslahar al'ummar Guinea, inda ya zargi gwamnatin Conde da cin hanci da rashawa da kuma take 'yancin ‘yan kasa.

Doumbouya ya yi alkawarin kafa gwamnatin rikon kwarya ta hadin kan kasa, sai dai bai fayyace lokaci da zai aiwatar da alkawarin ba.

Juyin mulkin da aka yi a Guinea dai shi ne na 4 cikin watanni 13 a Yammaci da kuma Tsakiyar Afirka, abin da ya tayar da hankalin masu sa ido kan yadda gwamnatocin da sojoji ke jagoranta ke karuwa a yankunan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.