Isa ga babban shafi
ECOWAS-Guinea

ECOWAS ta lafta wa Guinea takunkumi saboda juyin mulki

Taron da shugabannin kasashen yammacin Afirka mambobi a kungiyar Ecowas ko kuma Cedeao suka gudanar ta hoton bidiyo a jiya Laraba, ya sanar da sanya takunkumai da dama a kasar Guinea Conakry sakamakon juyin mulkin da aka yi wa Alpha Conde.

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo kuma shugaban kungiyar ECOWAS, yayin jagorantar taron kungiyar a birnin Accra.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo kuma shugaban kungiyar ECOWAS, yayin jagorantar taron kungiyar a birnin Accra. © Reuters
Talla

Ministan Harkokin Wajen Burkina Faso Alpha Barry, ya ce daya daga cikin matakan da taron ya dauka sun hada da dakatar da Guinea daga kasancewarta mamba a kungiyar ta Ecowas.

Kungiyar ta kuma bukaci sojoji su gaggauta sakin hambararren shugaba Farfesa Alpha Conde, tare da yanke shawarar tura tawaga ta musamman zuwa birnin Conakry don ganawa da sojojin da suka yi wannan juyin mulki a wannan Alhamis.

A lokacin da yake gabatar da jawabin bude taron a jiya, shugaban riko na kungiyar ta Ecowas wato shugaban Ghana Nana Akufo-Ado, ya bayyana juyin mulkin da cewa, ya saba wa dokokin kare dimokuradiyya da kyakkyawan jagoranci da kungiyar ta shimfida.

A daya bangare shugaban kasashen na yammacin Afirka, ya saurari rahoton tawagar mai shiga tsakani dangane da rikon kwaryar kasar Mali, tare da jaddada bukatar ganin an mutunta wa’adin watanni 18 don shirya sabbin zabuka na dimokuradiyya a kasar ta Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.