Isa ga babban shafi
Mali-ECOWAS

ECOWAS ta kakabawa manyan jami'an gwamnatin Mali takunkumai

Kungiyar ECOWAS ta sanya takunkumi kan jami’an gwamnatin rikon kwaryar Mali ciki har da Firaminista Choguel Kokalla Maiga amma kuma banda shugaban sojojin da ya jagoranci juyin mulkin kasar wato kanal Assimi Goita.

Firaminista Choguel Maïga na jerin wadanda takunkuman na ECOWAS ya shafa.
Firaminista Choguel Maïga na jerin wadanda takunkuman na ECOWAS ya shafa. AFP - KENA BETANCUR
Talla

Takunkuman na ECOWAS kamar yadda kungiyar ta sanar sun biyo bayan juyin mulkin da kasar ta gani har sau biyu a watan Agustan shekarar 2020 da kuma na watan Mayun bana baya matakin sojojin na kin cika alkawarin da suka dauka na gudanar da zabe ranar 27 ga watan Fabarairun 2022.

Firaminista Maiga ne babban jami’in da ke cikin jerin wadanda takunkuman na ECOWAS suka shafa sai kuma wasu ministocinsa 27 baya ga daidaikun mutane 121 da ke rike da mabanbantan mukamai a cikin gwamnatin rikon kwaryar kasar, galibinsu manyan hafsoshin Soji.

Kanal Assimi Goita, jagoran gwamnatin rikon kwaryar ta Mali kuma shugaban gungun sojojin da suka yi juyin mulki baya cikin jerin wadanda aka laftawa takunkumai haka zalika ministan harkokin wajen kasar Abdoulaye Diop.

Karkashin takunkuman dai an kwace dukkannin kadarorin wadanda aka kakaba wa takunkuman haka zalika an haramta musu yin balaguro zuwa ilahirin kasashen ECOWAS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.