Isa ga babban shafi

Ecowas na taro kan matsalolin da ke addabar Yammacin Afirka

A ranar wannan Lahadi ne, shugabannin kasashen mambobin kungiyar yankin Yammacin Afirka ta Ecowas suka fara gudanar da taron koli na kungiyar karo na 62 a birnin Abuja fadar gwamnatin Najeriya.

Wani taron Shugabanin ECOWAS a Accra  na kasar Ghana
Wani taron Shugabanin ECOWAS a Accra na kasar Ghana © Rfi hausa
Talla

Bayan rantsar da sabon shugaban Hukumar Gudanarwar kungiyar  Alieu Touray, sun shiga zauren taron a asirce domin tattauna batutuwa da dama da suka shafi yankin, da suka hada da juyin mulkin da aka samu a kasashen Mali, Burkina Faso da kuma Guinea Conakry.

Manzanni na musamman da kungiyar ta Ecowas/Cedeao ta nada don tattaunawa da sojojin da suka kwaci mulki a kasashen uku za su gabatar da rahotanninsu a gaban wannan taro na birnin Abuja.

Wasu batutuwa da taron na wannan Lahadi ke tattaunawa sun hada da sojojin Cote D’ivoire fiye da arba’in da mahukuntan Mali ke tsare da su bisa zargin shiga kasar a matsayin sojin haya, sai batun shirin samar da kudade na bai-daya a yankin da kuma yaki da ayyukan ta’addanci.

Hakazalika shugabannin kasashen yankin da ke halartar taron na Abuja, za su yi amfani da wannan dama domin dora tubalin farko na fara aikin gina sabuwar cibiyar kungiyar Ecowas wadda kasar China za ta gina wa kasashen matsayin kyauta a kan kudi dala milyan 32.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.