Isa ga babban shafi

An kai hare-haren ta'addanci sama da 1,800 a Yammacin Afirka a 2023 - ECOWAS

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ce za ta tattauna batun yadda za a karfafa rundunar tsaro a yankin don magance matsalar rashin tsaro da kuma barazanar juyin mulki.

Dakarun rundunar Barkhane mai yaki da ta'addanci a kasashen Mali, Nijar, Burkina Faso da Mauritania.
Dakarun rundunar Barkhane mai yaki da ta'addanci a kasashen Mali, Nijar, Burkina Faso da Mauritania. RFI/Coralie Pierret
Talla

Yammacin Afirka an samu bayanai kan hare-hare sama da 1,800 a cikin watanni shida na farkon shekarar 2023, wanda ya haifar da mutuwar kusan mutum 4,600 wanda hakan ya haifar da kalubale ga ayyukan jin kai sosai.

Omar Touray, babban jami’in kungiyar ta ECOWAS, ya shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talata cewa mutane sama da 500,000 daga kasashe 15 mambobin kungiyar, sun kasance ‘yan gudun hijira ne kuma kusan miliyan 6.2 sun rasa matsugunansu a cikin gida.

Ya kara da cewa, idan har kasashen duniya ba su kai dauki ga mutane miliyan 30 da ke bukatar abinci a yankin ba, adadin na iya karuwa zuwa miliyan 42 a karshen watan Agusta.

Touray, wanda shi ne shugaban hukumar ECOWAS, ya dora laifin kan manyan laifuka da ake aikatawa, kama daga ‘yan tawaye masu dauke da makamai, sauye-sauyen gwamnati da ba bisa ka’ida ba, matsalolin da suka danganci muhalli, da kuma yada labaran karya da ke haddasa rashin tsaro a yankin.

Ya ce yankin na cikin fargabar sake dawowar mulkin soja, inda kasashe uku wato Mali, Burkina Faso da Guinea ke karkashin mulkin soja.

Touray, wanda ya kasance tsohon ministan harkokin wajen Gambiya ya ce: "Sakamakon koma bayan da aka samu daga bangaren dimokuradiyya, shine ya haddasa rashin tsaron da yammacin Afirka da kuma Sahel ke fuskanta tun da dadewa."

Tsakanin watan Janairu zuwa 30 ga watan Yuni an kai hare-hare 2,725 a Burkina Faso, 844 a Mali, 77 a Nijar, da kuma hare-hare 70 a Najeriya wanda duk ya yi sanadin mutuwar mutane 4,593, a cewar Touray.

Ya kara da cewa hare-haren da ake kai wa a Benin da Togo wadanda ke da iyaka da Tekun Atlantika ‘yar manuniya ce kan yadda ayyukan ta’addanci ke kara karfi zuwa yankunan da bakin teku, lamarin da ke kara zama barazana ga yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.