Isa ga babban shafi

Mali ta yi watsi da shiga tsakanin ECOWAS wajen sakin Sojin Ivory Coast 46

Gwamnatin Mali ta yi watsi da kiran da kungiyar ECOWAS ta yi mata na sakin Sojojin Ivory Coast da ta ke tsare da su tun cikin watan Yulin inda ta yi gargadin amfani da kungiyar wajen katsalandan a harkokin shari’a da siyasar cikin gidan kasar.

Shugaban gwamnatin Sojin Mali, Kanal Assimi Goita.
Shugaban gwamnatin Sojin Mali, Kanal Assimi Goita. AFP - NIPAH DENNIS
Talla

Kakakin gwamnatin Sojin Mali, ya yi kakkausar suka ga matakin na ECOWAS yayinda ya bayyana cewa sam babu gaskiya a cikin zargin da Abidjan ta yiwa Bamako na kokarin yi mata barazana a sharuddan da ta gindaya mata gabanin sakin sojojin 46.

Alaka ta kara tsami tsakanin Ivory Coast da Mali ne bayan da Bamako ta ci gaba da tsare sojojin 46 dalilin da ya sanya Abidjan bukatar kungiyar ECOWAS ta shiga tsakani don sakin sojojin.

Sai dai martanin gwamnatin ta Sojin Mali game da bukatar, ya yi gargadi kan shigowar kungiyar ko kuma tsoma bakinta a lamurran cikin gidan kasashe, ta na mai cewa shiga tsakanin ta Togo ke yi kadai kasar za ta iya lamunta.

Tun ranar 10 ga watan Yulin shekarar nan ne Mali ta kame sojojin Ivory Coast 49 jim kadan bayan saukarsu a filin jirgin saman birnin Bamako, bisa zarginsu da kasancewa sojojin hayar da ke taimakawa ayyukan ta’addanci a kasar, duk da ikirarin da Abidjan ta yin a cewa sojojin na ta sun shiga kasar ne don taimakawa dakarun Majaliar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya.

Makwanni 3 da suka gabata ne gwamnatin Malin ta saki mata 3 da ke cikin sojojin yayinda ta bayyana cewa dole ne Ivory Coast ta mika mata ‘yan siyasar kasar da ke samun mafaka a wajenta don mika mata Sojin a wani yanayi mai kama da musayar fursinoni.

Sai dai wata majiya da ke da kusanci da gwamnatin Abidjan ta ce ECOWAS na shirin jagorantar wani taron gaggawa a mako mai zuwa don tattaunwa bukatar da Ivory Coast ta shigar a kokarin tilastawa Mali sakin Sojojin 46.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.