Isa ga babban shafi

Mali ta bukaci Ivory Coast ta fanshi Sojojinta da ke tsare a Bamako

Gwamnatin Sojin Mali ta amince da sakin ilahirin sojojin Ivory Coast da ta kame amma bisa sharadin mika mata wasu ‘yan siyasar kasar wadanda Abidjan ke bai wa mafaka, a matsayin fansa ko kuma diyyar sojin 46.

Shugaban gwamnatin sojin Mali Kanal Assimi Goita.
Shugaban gwamnatin sojin Mali Kanal Assimi Goita. © AFP
Talla

A watan Yulin da ya gabata ne mahukuntan Mali suka kame Sojin na Ivory Coast 46 jim kadan bayan saukarsu a filin jirgin saman birnin Bamako bisa zarginsu da kasancewa Sojin hayar da ke taimakawa wajen ta’azzara hare-haren ta’addanci a sassan kasar, lamarin da ya haddasa tsamin alaka tsakanin kasashen biyu makwabtan juna.

Ivory Coast na ci gaba da nanata cewa rashin adalci ne ci gaba da tsare Sojojin da Malin ke yi la’akari da cewa sun shiga kasar ne don taimakawa a yakin da dakarun Majalisar Dinkin Duniya ke yi da ayyukan ta’addanci.

Sai dai masu shigar da kara na Mali sun tuhumi sojojin da kasancewa barazana ga tsaron kasa wadanda ake hada hannu dasu don kaddamar da hare-haren ta’addanci a sassan Mali ko da ya ke tuni mahukuntan suka saki mata 3 da ke cikin tawagar sojojin wadanda suka koma gida a makon jiya.

Gwamnatin Sojin Mali dai a baya ta ce dole ne ayi sojojin shari’a tare da zartas musu da hukunci kan taimakon ta’addanci, amma a jiya juma’a jagoran gwamnatin Sojin ya sauya shawara da cewa a shirye Mali ta ke ta saki Sojojin amma da sharadin mika mata ‘yan kasarta da ke samun mafaka a Abidjan.

Cikin mutanen da Mali ke bukatar Ivory Coast ta mika mata har da Karim Keita da ga hambararren shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita da kuma Tieman Hubbert Coulibaly tsohon ministan tsaro da kuma ministan harkokin wajen kasar a lokacin mulkin Keita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.