Isa ga babban shafi

'Yan ta'addan Mali sun kashe gomman fararen hula yayin wani hari a Talataye

Gomman fararen hula ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare da kungiyoyin ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi suka kai kauyukan arewacin Mali a cikin makon da muke bankwana da shi.

Wasu 'yan ta'adda da ke ikirarin Jihadi a Mali.
Wasu 'yan ta'adda da ke ikirarin Jihadi a Mali. © AP/STR
Talla

A jerin hare-haren ‘yan ta’addan cikin makon nan, har da farmaki kan kauyen Talataye mai tazarar kilomita 150 daga birnin Gao na Mali, harin da ke matsayin irinsa na farko da ‘yan ta’addan ke kaiwa garin tun bayan farowar hare-haren fiye da shekaru 10 da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa gabanin kaddamar da farmakin sai da bangarorin ‘yan ta’addan 3 da suka kunshi ISGS da GSIM da ke matsayin reshen Al-Qada da kuma MSA suka gwabza fada da junansu a talatar da ta gabata.

Wasu ganau sun shaidawa AFP cewa bangarorin 3 sun dauki akalla sa’o’I 3 suna musayar wuta da juna gabanin farwa garin na Talataye tare da kisan dimbin fararen hular.

Shaidu sun bayyana AFP cewa mayakan ISGS sun kwace iko da garin yanzu haka yayinda aka shiga wani yanayi na firgici da yah ana iya samun cikakken bayan ikan halin da ake ciki a Talataye.

Alkaluman da ganau suka baiwa, AFP sun nan ta ke sai da mayakan na ISGS suka kashe fararen hula 45 yayinda wasu majiyoyi ke cewa alkaluman za su iya ninkawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.