Isa ga babban shafi

Gwamnatin Mali ta sako wasu daga cikin sojojin Cote d'Ivoire da take tsare da su

Hukumomin kasar Togo sun sanar da sakin wasu sojojin kasar Cote d'Ivoire mata guda uku da ake tsare da su a Mali tun watan Yuli.

Shugaban gwamnatin sojin Mali kenan, Kanal Assimi Goita
Shugaban gwamnatin sojin Mali kenan, Kanal Assimi Goita AP
Talla

An saki sojojin ukun ne bisa dalilai na jin kai kuma suna cikin rukunin sojojin Ivory Coast 49 da aka tsare a Bamako tun ranar 10 ga watan Yuli.

Togo dai na shiga tsakani a rikicin Mali da Cote d'Ivoire, inda a yanzu haka ake ci gaba da tattauna kan batun sakin sauran sojoji 46 da suka rage.

A cewar hukumomin kasar Mali, ana zargin sojojin Ivory Coast da kasancewa sojojin haya yayin da hukumomin Ivory Coast ke ikirarin cewa suna gudanar da aikin tallafawa dakarun MDD a Mali.

Hukumomin Ivory Coast sun yi alkawarin bin ka'idojin Mali da na Majalisar Dinkin Duniya dangane da girke dakarun soji a kasar.

Kasar Mali ta kuma zargi gwamnatin Abidjan da tunzura kasashen yammacin Afirka wajen tsaurara takunkumi kan sojojin Mali da suka yi juyin mulki sau biyu tun shekara ta 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.