Isa ga babban shafi

Sojojin Mali da na ketare sun kashe fararen hula 50 tare da kame wasu 500- MDD

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bankado yadda Sojojin Mali da hadin gwiwar Sojin ketare da ke taimakon kasar a yaki da ayyukan ta'addanci, suka hallaka fararen hula akalla 50 tare da kame wasu fiye da 500 a wani sumame da suka kaddamar cikin watan Aprilun da ya gabata.

Wasu Sojoji a yankin Gao na Mali.
Wasu Sojoji a yankin Gao na Mali. AP - Jerome Delay
Talla

Rahoton wanda Majalisar ta fitar a jiya laraba ta ce Sojin sun aikata kisan ne lokacin da fararen hula ke tsaka da cin wata kasuwa a yankin Hombori a tsakiyar lardin Douentza, bayan da motar ayarin Sojin ta taka nakiya a kan hanya gab da wajen.

Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya MINUSMA ta bayyana cewa cikin wadanda Sojin suka kashe har da wata da danta, lamarin da ke nuna tsantsar cin zarafi da take hakkin dan adam.

Wannan dai ba shi ne karon faro da Majalisar Dinkin Duniya ke zargin sojin na Mali da kisan fararen hula ba, a yakin fiye da shekaru 10 da kasar ta shafe ta na yi da mayaka masu ikirarin jihadi da ke da alaka da kungiyoyin Al Qaeda da IS.

Duk da cewa kai tsaye rahoton Majalisar bai kama sunan Sojoji farar fatar da ake zargi da taimakon Sojin na Mali wajen aikata kisan ba, amma kai tsaye bayanan da ke kunshe cikin rahoton na alakanta laifin na Sojojin hayar kamfanin Wagner na Rasha da ke aiki a kasar.

Tun bayan juyin mulkin da Sojoji suka yi a Mali cikin shekarar 2020 kasar ta karfafa shirin yaki da ayyukan ta'addanci ta hanyar dauko Sojojin haya daga Rasha don taimaka mata, sai dai matakin ya fuskanci kakkausar suka daga manyan kasashen Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.