Isa ga babban shafi

Sahel: Burkina Faso da Nijar sun bukaci Mali ta koma shirin hadin gwiwar soji

Kasashen Burkina Faso da Nijar da ke fama da rikicin mayakan jihadi da ya barke a arewacin kasar Mali a shekarar 2013, sun yi kira ga gwamnatin Bamako da ta ci gaba da daukar nauyin da ya rataya a wuyanta na aikin hadin gwiwa wajen yakar masu tayar da kayar baya.

Mayakan jihadi dai na ci gaba da kai hare-haren a yankin Sahel na Afirka
Mayakan jihadi dai na ci gaba da kai hare-haren a yankin Sahel na Afirka AFP - PIUS UTOMI EKPEI
Talla

A tsakiyar watan Mayu, hukumomin rikon kwarya na kasar Mali, suka yanke shawarar ficewa daga kungiyar G5 Sahel da kuma rundunar hadin gwiwa, abin da ya kasance kawancen soja da ke yaki da kungiyoyin masu jihadi, tare da kasashen Mauritania, Chadi, Burkina da Nijar.

Ministan tsaron Nijar, Alkassoum Indattou ya ce sun yi nazari kan halin da ake ciki a yankin kuma mun yi lura da cewa Mali a yanzu ita ce babbar kasa da ba ta cikin shirin na hadin gwiwar tsaro.

Indattou, tare da rakiyar takwaransa, ministan tsaron Burkina Faso, Janar Barthélemy Simporé, na magana ne bayan wata ganawa da shugaban rikon kwarya na Burkina Faso, Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo.

Mista Indattou, tare da rakiyar takwaransa, ministan tsaron Burkina Faso, Janar Barthélemy Simporé, na magana ne bayan wata ganawa da shugaban rikon kwarya a Burkina Faso, Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo.

Daga ranar 2 zuwa 25 ga watan Afrilu, sojojin bangarorin biyu sun gudanar da wani samame na hadin gwiwa mai suna Taanli 3 alliance a harshen Gulmacema da ake magana da shi a gabashin Burkina Faso wanda ya yi sanadin kawar da 'yan ta'adda dari.

Burkina Faso da makwabciyarta Nijar sun shafe shekaru da dama suna fuskantar hare-haren masu jihadi akai-akai, wadanda ake danganta su da kungiyoyin jihadi masu alaka da kungiyar IS da kuma al-Qaeda.

Hare-haren mayakan dai sun yi sanadin mutuwar dubban mutane a kasashen biyu tare da raba dubbai da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.