Isa ga babban shafi

Mali ta yi watsi da zargin Majalisar Dinkin Duniya kan kisan fararen hula 50

Gwamnatin Sojin Mali ta yi watsi da rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan zargin dakarun kasar da taimakon Sojin hayar Wagner da kisan fararen hula 50 cikin watan Aprilun da ya gabata.

Shugaban gwamnatin sojojin kasar Mali Kanal Assimi Goita.
Shugaban gwamnatin sojojin kasar Mali Kanal Assimi Goita. AP - Baba Ahmed
Talla

Rahoton wanda Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a larabar nan, ta zargi Sojin na Mali da taimakon wasu sojojin ketare da bata fayyace ko su wanene ba, da laifin kai wani sumame kasuwar kauye tare da kisan fararen hular da kuma kame wasu fiye da 500.

Martanin da gwamnatin Sojin ta Mali ta fitar ta ce rahoton na Majalisar Dinkin Duniya bai dogara da wata hujja guda da ke nuna kanshin gaskiyar faruwar abin da ake zargin ba.

Ma’aikatar harkokin wajen Mali ta ce Majalisar ta fitar da rahoton ne da kashin kanta kan bayanai da aka bata ba tare da gudanar da bincike ba, haka zalika ba ta da hujja ko guda kan zargin da ta ke.

Sanarwar da ma’aikatar wajen ta fitar wadda aka yadata a shafukan sada zumunta, ta alakanta rahoton majalisar da bayanai daga hannun kungiyoyin ‘yan ta’adda da gwamnatin ke aikin kakkabe su a sassan kasar.

Manyan kasashe da ita kanta Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da nuna adawa da salon da Mali ke amfani da shi wajen yaki da matsalar ta’addancin da ta dabaibayeta, musamman bayan korar dakarun ketare da ta zarga da taimakon ayyukan ta’addancin da kuma dakko sojojin hayar Rasha na kamfanin Wagner.

Mali wadda ke karkashin mulkin Soji tun cikin shekarar 2020 bisa jagorancin Assimi Goita ta bayyana sojojin na Rasha a matsayin masu baiwa dakarunta horo na musamman.

A ranar 15 ga watan Agustan da ya gabata ne tawagar karshe ta Sojin Faransa ta kammala ficewa daga kasar ta Mali bayan tsamin alaka tsakanin kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.